Mista Lucky Aiyedatiwa ya karbi rantsuwa a matsayin sabon Gwamnan Jihar Ondo, ’yan sa’o’i bayan rasuwar Gwamna Rotimi Akeredolu.
Babban Alƙalin Jihar Ondo, Mai Shari’a Olusegun Odusola, ne ya ba wa Aiyedatiwa rantsuwar fara aiki a matsayin sabon gwamna.
Lucky Aiyedatiwa shi ne mataimakin Akeredolu kuma ya kasance mukaddashin gwamna tun ranar 13 ga watan Disamba a sakamakon tsanantar rashin lafiyar Akeredolu.
- Ghali Na’Abba: Muhimman Abubuwa 10 da ya kamata ku sani
- Dalibar da ke kai wa ’yan bindiga rahoto ta shiga hannu
A safiyar Larabar nan Gwamna Akeredolu ya rasu a kasar Jamus inda ake jinyar sa, saboda cutar kansar jini da yake fama da ita.
Akeredolu wanda ya rasu a wa’adin mulkinsa na biyu ya shafe watanni uku — daga Satumba zuwa Nuwambar 2023 — yana jinya a kasar Jamus.
Bayan dawowarsa kuma ya tare a birnin Ibadan na jihar Oyo, inda daga nan yake gudanar da harkokin mulki.
Yanayin rashin lafiyarsa a zamansa a Ibadan ya haifar da ce-ce-ku-ce har wasu suka bukaci ya bar wa mataimakin nasa ya ci gaba da jan ragamar jihar.
A baya-bayan nan lamarin ya tayar da kura da zargin mataimakin har ta kai ga neman tsige shi.
Wata sabuwar sarƙaƙiya ita ce yadda ake zargin wasu jami’ai na amfani da sa hannun Akeredolu na bogi.