Tsohon Gwamnan Jihar Edo, Adams Oshiomhole, ya kare zabin Musulmai biyu a matsayin ’yan takarar jam’iyyar, inda ya ce a baya zabin Musulmi da Kirista bai tsainana wa Najeriya komai ba.
Ya ce lokaci ya yi da Najeriya za ta yi watsi da banbancin addini, kabilanci da na yanki, ta koma duba cancanta da kwarewa don kai ta tudun mun-tsira.
Da yake tattaunawa da gidan talabijin na TVC ranar Alhamis, Oshiomhole, wanda kuma tsohon Shugaban jam’iyyar APC na kasa ne, ya yaba da zabin Musulmai biyu a matsayin ’yan takarar, inda ya ce Tinubu ya yi abin da ya dace.
A makon da ya gabata ne dan takarar Shugaban Kasa na APC, Bola Ahmed Tinubu ya ayyana sunan tsohon Gwamnan Jihar Borno, Sanata Kashim Shettima a matsayin Mataimakinsa a takarar a zaben na 2023.
A cewar Oshiomhole, “Duk lokacin da jam’iyyun hamayya suka fara magana a kan zabin Musulmai biyu, a lokacin nake dada gamsuwa cewa matakin Tinubu a kan daidai yake.
“An yi abin da ya dace. Mun jima muna fama da matsalar banbancin addini a ’yan shekarun nan. Matakin da Tinubu ya dauka na nuni da cewa zai rika bugar kriji yana yin abin da ya dace idan aka zabe shi.
“Da a ce yawan majami’u da masallatan da muke ginawa sun kai yawan masana’antunmu, da ba mu tsinci kanmu a cikin irin halin talaucin da muke ciki ba,” inji shi.
Ya kuma ce ya gamsu da zabin Sanata Shettima saboda kwarewarsa da kuma tarihin abubuwan da ya aiwatar a baya.
Dangane da batun zargin da ake yi cewa Tinubu da Mataimakin nasa za su ‘Musuluntar’ da Najeriya, ya ce bai ga ta yadda za a yi Tinubun da ya gaza Musuluntar da iyalansa zai yi nasarar yin haka a Najeriya ba.
“Meye abin tsoro a wannan fargabar da wasu suke yi? Sun ce akwai barazanar za su Musuluntar da Najeriya. Shi kansa dan takarar (Tinubu), ya Musuluntar da iyalansa ne? Matarsa fa Kirista ce kuma Fasto?” inji Oshiomhole.