✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Kenya: Dan takara ya yi harbi da bindiga a rumfar zabe

Rahotanni daga kasar Kenya, wacce ta gudanar da zaben Shugaban Kasa ranar Talata na nuna ba a kwashe da dadi ba a wasu yakunana kasar…

Rahotanni daga kasar Kenya, wacce ta gudanar da zaben Shugaban Kasa ranar Talata na nuna ba a kwashe da dadi ba a wasu yakunana kasar da kuma tasoshin zabe.

A wani rahoto da BBC ta wallafa, ta ce an sami rahotannin tashe-tashen hankula a wasu wuraren da aka gudanar da zaben.

Wani dan majalisar kasar mai suna Didimus Barasa ya harbe wani hadimin abokin karawarsa na zabanen kujerar majalisar kasar a zaben da aka gudanar.

Dan majalisar da ake zargi da yin harbin dai shi ne ke wakiltar yankin Kimili, kuma tun da ya yi harbin a yammacin Bungoma, ya yi batan dabo.

Babban mai gabatar da kara na kasar ya bayar da umarnin a kama Mista Barasa a duk inda aka gan shi.

A wani labarin kuma wani dan takarar majalisar kasar ya fito da bindiga a wurin jefa kuri’a a gudumar Siaya da ke kudancin kasar.

Hukumomin kasar sun dukufa wajen binciken yadda aka yi, wani mutum ya rasa ransa a Eldoret bayan wata hatsaniya tsakaninsa da wani fitaccen dan kasuwa da ya tsaya takarar kujerar Gwamnan yankin.

An dai kammmla zaben ne a ranar Talata yayin da ake ci gaba da jiran sakamakon Shugaban kasa da na ’yan majalisar kasar