Rahotanni daga kasar Kenya, wacce ta gudanar da zaben Shugaban Kasa ranar Talata na nuna ba a kwashe da dadi ba a wasu yakunana kasar da kuma tasoshin zabe.
A wani rahoto da BBC ta wallafa, ta ce an sami rahotannin tashe-tashen hankula a wasu wuraren da aka gudanar da zaben.
- Masu yada labaran karya a Intanet za su gamu da azabar Allah – Umar Sani Fagge
- An kama mai shekara 70 kan luwadi da yaro mai shekara 12
Wani dan majalisar kasar mai suna Didimus Barasa ya harbe wani hadimin abokin karawarsa na zabanen kujerar majalisar kasar a zaben da aka gudanar.
Dan majalisar da ake zargi da yin harbin dai shi ne ke wakiltar yankin Kimili, kuma tun da ya yi harbin a yammacin Bungoma, ya yi batan dabo.
Babban mai gabatar da kara na kasar ya bayar da umarnin a kama Mista Barasa a duk inda aka gan shi.
A wani labarin kuma wani dan takarar majalisar kasar ya fito da bindiga a wurin jefa kuri’a a gudumar Siaya da ke kudancin kasar.
Hukumomin kasar sun dukufa wajen binciken yadda aka yi, wani mutum ya rasa ransa a Eldoret bayan wata hatsaniya tsakaninsa da wani fitaccen dan kasuwa da ya tsaya takarar kujerar Gwamnan yankin.
An dai kammmla zaben ne a ranar Talata yayin da ake ci gaba da jiran sakamakon Shugaban kasa da na ’yan majalisar kasar