A yayin da ake ci gaba da gudanar da zaben Kananan Hukumomi a Jihar Kano, wasu matasa rataye da katin jam’iyyar APC a wuyansu sun yi awon gaba da takardun kada kuri’a da kuma akwatinan zabe a Karamar Hukumar Ungogo.
Lamarin dai ya faru ne sanyin safiya a mazabar Tudun Fulani, akwatin Jamade da ke Karamar Hukumar.
- Rikici ya barke tsakanin Matafiya da Ma’aikatan Jirgin sama a Kano
- An girke jami’an tsaro 10,000 domin zaben kananan hukumomin Kano
Rahotanni sun nuna cewa mutane biyu ne kacal aka bari suka kada kuri’a a wurin kafin a yi awon gaba da kayan zaben.
Sai dai ko da mutanen suka dawo da kayan zaben da misalin karfe 11:30 na safe, sai suka sanar da cewa an kammala zaben.
Daga nan ne kuma sai aka ga wakilin jam’iyyar APC ya fice tare da sauran malaman zabe daga wurin.
An dai jiyo daya daga cikin matasan da suka yi awon gaba da kayan zaben yana cewa tun da mutane ba za su fito su yi zaben ba, su za su yi musu.
An yi dangwale
A wani labarin kuma, a wata mazaba da ke unguwar Brigade a Mazabar Gama ta Karamar Hukumar Nassarawa, wakilan Aminiya sun lura da yadda wata jam’iyya take dangwale kuri’un.
Masu dangwalen dai sun yi rika yi ne a fili, yayin da suke barazanar hukunta duk wanda suka gani yana kokarin daukar hotonsu.
Kazalika, an samu makamancin wannan ma a mazabar Kafin Agur.