✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Kano: APC ta roki a yi azumi ta samu nasara a kotu

A ranar Asabar ne jam'iyyar NNPP ta gudanar da taron addu'ar neman nasara a kotun sauraren kararrakin zabe.

Jam’iyyar APC a Jihar Kano ta umarci ’ya’yanta da sauran magoya baya da su gudanar da azumi da addu’o’i domin neman taimakon Allah wajen samun nasara a kotun sauraren kararrakin zaben gwamna.

Sakataren jam’iyyar, Ibrahim Zakari Sarina ne, ya shaida wa Aminiya hakan a ranar Litinin, inda ya ce tuni akasarin magoya bayansu suka fara azumi a lokacin da suke gudanar da addu’o’i a unguwanni da kananan hukumomi daban-daban.

Aminiya ta ruwaito cewa hakan na zuwa ne bayan da babbar abokiyar hamayyar jam’iyyar, NNPP ta gudanar da wani taron addu’a a ranar Asabar, tana mai neman nasara daga Allah kan sakamakon hukuncin kotun da ake dako a jihar.

Sarina ya ce, “Kamar yadda kuka sani, mu ‘yan dimokuradiyya ne kuma ba mu yarda da jerin gwano ko wani abu da zai yi kama da kungiyar asiri ba.

“Duba da yanayin tattalin arzikin kasar nan, mun umarci duk wanda zai iya yin azumin a yau (Litinin) ya yi.”

Ya kara da cewa an karkasa zaman taron addu’o’in a matakin unguwanni da kananan hukumomi domin a samu kulawa da kaucewa duk wani tashin-tashina.

“An gudanar da tarukan addu’o’in ne a matakin unguwanni da kananan hukumomi da kuma ofisoshin yakin neman zabenmu da ke fadin jiha.

“Ba ma son yanayin da mutane za su sha wahala. Muna son a zauna lafiya da tsari. Kazalika a yau, ina hanyar tafiya zuwa kauyena don yin addu’a a can,” in ji shi.

Aminiya ta ruwaito cewa al’amura sun yi zafi a Jihar Kano tun bayan da wata mai shari’a Flora Azinge ta yi korafin cewa wasu lauyoyi sun yi kokarin bata cin hanci don sauya hukuncin da ta ke shirin yankewa.

Sai dai hakan ya haifar da zarge-zarge da zage-zage tsakanin APC da NNPP a jihar.