✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Kananan Hukumomi: ’Yan daba sun yi awon gaba da na’urorin zabe 41 a Kaduna

An sace na’urorin ne a Kananan Hukumomin Giwa da Igabi.

Akalla na’urorin kada kuri’a guda 41 ne ’yan daba suka yi awon gaba da su yayin zaben Kananan Hukumon Jihar Kaduna na ranar Asabar.

Shugabar Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kaduna (KADSIECOM), Saratu Audu-Dikko ce ta tabbatar da hakan yayin zantawarta da maneman labarai a Kaduna ranar Asabar.

Ta ce an sace na’urorin ne a Kananan Hukumomin Giwa da Igabi.

Shugabar ta ce adadin bai ma kunshi na’urorin da ’yan dabar suka lalata yayin zaben ba.

Ta kara da cewa, “An sace na’urori guda 31 a gundumar Kwarau da ke Karamar Hukumar Igabi, sannan aka lalata guda biyu, yayin da a Panhauya kuwa da ke Karamar Hukumar Giwa aka lalata guda tara.

“Kazalika, ’yan dabar sun kuma yi awon gaba da kayan zabe tare da dukan malamin zabe da kuma direban da ke dauke da kayan,” inji ta.

Shugabar hukumar ta kuma ce akwai wasu ma’aikatan hukumar da suma aka daka, ciki har da na wucin gadi. (NAN)