✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Kaduna: PDP ta lashe a Karamar Hukumar Jaba

Dan takarar PDP ya lashe zaben bayan samun kuri'u mafi rinjaye.

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kaduna ta bayyana Mista Phillip Gwada na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar shugabancin Karamar Hukumar Jaba da aka gudanar a ranar Asabar.

Jami’in tattara sakamakon zaben, Farfesa Peter Omale, shi ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a ofishin hukumar zaben.

Omale ya ce Gwada ya samu kuri’a 9,012 inda ya kayar da dan takarar jam’iyyar APC, Benjamin Jock, wanda ya samu kuri’a 5,640.

Ya ce dan takarar jam’iyyar ADP, Alhamdu Gyet, shi ne ya zo na uku da kuri’a 2,732.

“Mista Phillip Gwada na PDP, bayan ya cika ka’idojin doka kuma ya sami kuri’u mafi rinjaye, an tabbatar da shi a matsayin wanda ya lashe zaben,” inji Omale.

Yanzu haka ana ci gaba da tattara sakamakon zaben kananan hukumomin da aka gudanar, inda hukumar zaben ke bayyana wadanda suka yi nasara.