Dan takarar Shugaban Kasar Iran mai ra’ayin rikau, Ebrahim Rais, ya kama hanyar lashe zaben bayan da aka kirga kashi 90 na kuri’un da aka kada.
Ma’aikatar Harkokin Cikin Gidan kasar ta sanar a safiyar Asabar cewa Ebrahim Rais, ya samu gagarumin rinjayen da zai yi matukar wahala sauran ’yan takarar su iya kamo shi; Har yanzu ba a sanar da shi a matsayin wanda ya yi nasara a hukumance ba.
- Buhari ya nemi MTN ya rage kudin data da kira
- An kama mutum 44 masu hada baki da ’yan bindigar Zamfara
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta ce, Ebrahim Rais, mai shekara 60, wanda a halin yanzu yake jagorantar sashen shari’ar kasar, ya samu kuri’a fiye da miliyan 17.8 daga cikin 28.6 da aka kidaya.
Tun da farko, a safiyar ta Asabar din, uku daga cikin ’yan takarar sun amince da shan kaye a hannun Raisi, wanda dan amshin shata ne ga Jagoran Addinin kasar, Ali Hosseini Khamenei.
Dama can ana kyautata zaton shi ne zai lashe zaben na ranar Juma’ah duk da karancin fitowar masu kada kuri’a da kuma haramta wa ’yan takara da dama shiga zaben.
Shi ma dan takara mai ra’ayin mazan-jiya, Mohsen Rezaei, tsohon Kwamandan Dakarun Juyin Juya Halin Musulunci, ya samu fiye da kuri’u miliyan 3.3.
Wanda ya biyo shi a baya shi ne tsohon Shugaban Babban Bankin kasar, Abdolnaser Hemmati, wanda shi ne kadai dan takara mai matsakaicin ra’ayi a zaben da ya samu kuri’a fiye da miliyan 2.4.
Sannan wani dan ra’ayin mazan jiyan kuma dan majalisar kasar, Amir Hossein Ghazizadeh Hashemit ya samu kuri’u fiye da miliyan daya.
Tun da farko, Shugaban Iran mai barin gado, Hassan Rouhani ya taya murna ga zababben Shugaban Kasar amma ba tare da ya ayyana sunan Raisi ba.