Wakilan Majalisar Dinkin Duniya da na kasar Iran da ke tattaunawa a kan shirin Nukiliyar kasar sun cimma wata matsaya da za ta sa a duba yuwuwar sake dawo da yarjejeniyar 2015 da ta wargaje.
Tuni dai Rafael Grossi, Shugaban Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) ya isa birnin Tehran na kasar ta Iran don tattaunawa da takwaransa na kasar, Mohammad Eslami ranar Lahadi.
- Ba daidai ba ne a katse hanyoyin sadarwa a Zamfara da Katsina – SERAP
- Yadda na kirkiri yin shayi a tanki da bututu – Rabilu mai shayi
Wannan dai ita ce tafiyar shugaban na IAEA zuwa Tehran ta farko tun bayan kama mulkin Shugaba Ebrahim Raisi wanda ya nada Eslami shugabancin hukumar a watan Agustan da ya gabata.
Duka bangarorin biyu dai sun bayyana tattaunawar a matsayin wacce ta yi nasara kuma sun amince su ci gaba da tattaunawar a gefen babban taron hukumar da zai gudana a birnin Vienna na Austria a cikin watan Satumbar nan.
Kazalika, sun kuma amince cewa Mista Grossi zai je Tehran nan ba da jimawa ba domin aikin sake na’urorin daukar hoto da na nadar bayanai da ke tashar inganta makamashin Nukiliyar ta Iran, kamar yadda yake a wata sabuwar dokar da Majalisar Dokokin kasar ta amince da ita a watan Disambar bara.
Tun a watan Fabrairu ne dai Iran ta amince cewa za ta mika na’urorin nadar bayanan ga hukumar bayan wata yarjejeniya da ta cimma a birnin Vienna wacce za ta kai ga dage takunkumin karya tattalin arzikin da Amurka ta kakaba mata.
Tattaunawar dai na zuwa ne kwana biyu bayan wasu sabbin rahotannin sirri na hukumar ta IAEA da suka bulla ta kafafen yada labarai da ke nuna shakkunta kan shirin na Iran.
Sai dai kasar ta tsaya kai da fata shirinta na inganta ma’adinin Uranium na zaman lafiya ne ba na kera makaman Nulkiliya ba.