✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Gwamnan Kogi: INEC ta fara raba takardun zabe

A shirin zaben Gwamnan Kogi da za a yi ranar Asabar Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC a yau Alhamis ta fara rabon…

A shirin zaben Gwamnan Kogi da za a yi ranar Asabar Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC a yau Alhamis ta fara rabon kayan zabe masu muhimmanci a duk cibiyoyin zaben Kananan Hukumomi 21 na jihar.

Wakilin AMINIYA da ke ofishin babban bankin Najeriya CBN da ke Lokoja babban birnin jihar Kogi, inda ake rabon kayan zaben. Ya ce, an raba takardun kada kuri’a da takardar rubuta sakamakon zaben a kananan Hukumomi 16 yanzu haka.

Takardun zaben Gwamnan Kogi lokacin da ake rabon su