Tsohon Shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya gargadi ’yan takarar shugabancin kasar Ghana game da rikici a yayin babban zabe mai zuwa a ranar 7 ga watan Disambar 2020.
Obasanjo ya yi wannan kira ne cikin wata wasika da ya aike wa da ’yan takarar jam’iyyun National Democratic Congress (NDC) da New Patriotic Party (NPP), inda ya ce yana da kyau su fahimci juna, domin samun zaman lafiya.
- Tsohon Shugaban Ghana Jerry Rawlings ya rasu
- Musulmin Ghana sun yi tattakin neman a yi zabe lafiya
- Sarkin Zazzau ya taimaka wa mulkina —Obasanjo
A shekara ta 2016 Akufo-Addo, ya kayar Mahama a zaben shugabancin kasar da ya gudana, yanzu ma za su sake karawa a babban zabe mai zuwa.
Yayin da zaben yake kara tunkarowa, Obasanjo ya bukaci ’yan takarar da su rungumi zaman lafiya, domin kauce wa tashin hankali a yayin zaben mai zuwa.
Daga karshe tsohon shugaban kasar, ya yi fatan alheri ga ’yan takarar shugabancin kasar Ghana da kuma samun zaman lafiya mai dorewa.