✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zaben Edo: Buhari ya ba Ize-Iyamu tutar takarar APC

Ize-Iyamu ya karbi tutar takarar gwamnan APC a jihar Edo bayan ganawa a Fadar Aso Rock da ke Abuja

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya mika wa Osagie Ize-Iyamu tutar tsayawa takarar gwamnan jam’iyyar APC a zaben Jihar Edo.

Buhari ya ba da tutar ne bayan ganawarsu a Fadar Shugaban Kasa gabanin kaddamar da yakin neman zaben Ize-Iyamu a ranar Asabar.

Taron na ranar Juma’a ya karbi bakuncin shugaban kwamitin yakin neman zaben Ize-Iyamu, Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje.

Sauran su ne Shugaban Kwamitin Rikon Jam’iyyar na Kasa kuma Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni na daga cikin mahalarta zaman.

Kazalika Shugaban Kungiyar Gwamnonin Jam’iyyar APC, Gwamna Atiku Bagudu na Jihar Kebbi, ya samu halartar zaman.

Babu tabbacin makasudin ziyarar amma ana hasashen Buni da Ganduje sun kai Ize-Iyamu ne domin gabatar da shi ga shugaban kasar, gabanin kaddamar da yakin neman zaben jam’iyyar ranar Asabar.