Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, ya maka dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal da kuma ita kanta jam’iyyar a kotu.
Wannan na zuwa ne baya zaben fidda-gwani da aka gudanar a Abuja, inda Tamnuwal a lokacin da yake jawabi ga wakilan jam’iyyar da su zabe shi, amma daga bisani ya janye wa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku, takararsa.
- Kotu ta ci Shugaban ’Yan Sanda tarar N1m kan baje-kolin wanda ake zargi
- Fashin zuwa aiki ya janyo wa ’yan NYSC 5 maimatawa a Sakkwato
A zaben fidda-gwanin Atiku ya samu kuri’u 371 wanda hakan ya sa ya yi nasara, yayin da Wike ya samu 237 a matsayin na biyu.
Tun bayan kammala zaben fidda-gwani na PDP ne dai Wike da magoya bayansa ke takun-saka da magoya bayan Atiku.
Bayan da aka dauki tsawon lokaci ana rikicin jam’iyyar, Wike da wani jigo a PDP, Newgent Ekamon a yanzu sun maka Atiku, Tambuwal da PDP kara a kotu, tare da mika sammaci mai lamba FHC/ABJ/CS/782/2022, ga wadanda ake kara.
A sammacin, an sanya PDP a matsayin wanda ake kara ta farko, sai Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) a matsayi wadda ake kara ta biyu, Tambuwal da Atiku a matsayin na uku da na hudu.
Daga cikin batutuwan da aka lissafo, Wike da Ekamon sun nemi kotun da ta umarci INEC da ta hana Atiku takara a zaben shugaban kasa na 2023.
Tuni aka fara rade-radin cewa Gwamna Wike na shirin ficewa daga jam’iyyar PDP.
Wasu rahotanni sun ce an cire tutocin ofishin Jam’iyyar PDP a Jihar Ribas, lamarin da ya haifar da yamutsi aka shiga tunanin ko maganar shirye-shiryen ficewar Wike daga PDP na dab da faruwa.