✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben cike gurbin Majalisar Dokokin Zamfara bai kammala ba – INEC

Hukumar Zabe ta Kasa mai Zaman Kanta INEC, ta ayyana cewa zaben cike gurbi na dan Majalisar Dokokin jihar Zamfara da aka gudanar ranar Asabar…

Hukumar Zabe ta Kasa mai Zaman Kanta INEC, ta ayyana cewa zaben cike gurbi na dan Majalisar Dokokin jihar Zamfara da aka gudanar ranar Asabar a Karamar Hukumar Bakura ta jihar Zamfara bai kammala ba.

Alkalin zaben, Farfesa Ibrahim Magawata ne ya sanar da hukuncin hakan biyo bayan soke sakamakon rumfunan zabe guda 14 na gundumar Bakura mai kuri’u 11,429.

Farfesa Magawata ya sanar cewa dan takarar jam’iyyar APC, Alhaji Bello Dankande Gamji ya samu kuri’u 16,464 yayin da Alhaji Ibrahim Tudu, dan takarar jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 18,645.

Ya kuma ce za a sanar da ranar da za a sake gudanar da zaben a wuraren da aka soke nan ba da dade wa ba.