✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Bayelsa: ’Yan sanda sun yi alkawarin samar da cikakken tsaro

Rundunar ‘yan Sandan jihar Bayelsa ta ce, za ta tabbatar da cikakken tsaro yayin zaben Gwamnan jihar da za a yi gobe Asabar. Kakakin rundunar…

Rundunar ‘yan Sandan jihar Bayelsa ta ce, za ta tabbatar da cikakken tsaro yayin zaben Gwamnan jihar da za a yi gobe Asabar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar SP Asnim Butswat, ne ya bayyana hakan yayin da yake tattaunawa da Kamfanin Dillanci Labarai NAN yau Juma’a a Yenogoa babban birnin jihar.

SP Asnim, ya kara da cewa, a yanzu haka rundunar ta kammala duk shirinta na hanyoyin gudanar da zabe cikin lumana. Ya kuma bukacki ‘yan siyasar jihar da su kiyaye doka don taimakawa jami’an tsaro wajen gudanar da ayyukan su.