✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Anambra: YPP da PDP sun lashe Kananan Hukumomi dai-daya da kyar

APGA dai ta lashe 13 daga cikin Kananan Hukumomi 15 din da aka bayyana.

Yayin da ake ci gaba da tattara sakamakon zaben Gwamnan Jihar Anambra na ranar Asabar, ya zuwa yanzu dai jam’iyyun YPP da PDP sun lashe Karamar Hukuma dai-daya daga cikin Kananan Hukumomi 15 din da aka bayyana.

Hakan dai na nufin dan takarar jam’iyyar APGA, Farfesa Charles Soludo shi ne ke kan gaba inda ya lashe Kananan Hukumomi 13 da Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC) ta bayyana sakamakonsu.

Karamar Hukumar da dan takarar YPP, Ifeanyi Ubah, ya fito, Nnewi ta Arewa ita ce ya lashe da kuri’a 6,485, yayin da Farfesa Soludo ya sami 3,369.

Kazalika, a Karamar Hukumar Ogbaru ma, dan takarar PDP, Valentine Ozigbo ne ya lashed a kuri’a 3,445, sai APGA da ke biye masa baya da kuri’a 3,051.