Yayin da ake ci gaba da tattara sakamakon zaben Gwamnan Jihar Anambra na ranar Asabar, ya zuwa yanzu dai jam’iyyun YPP da PDP sun lashe Karamar Hukuma dai-daya daga cikin Kananan Hukumomi 15 din da aka bayyana.
Hakan dai na nufin dan takarar jam’iyyar APGA, Farfesa Charles Soludo shi ne ke kan gaba inda ya lashe Kananan Hukumomi 13 da Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC) ta bayyana sakamakonsu.
- ‘Ba don karba-karba ba, da sai Arewa ta shekara 300 tana mulki’
- Zaben Anambra: Jami’in INEC ya tsere da takardun sakamakon zabe guda 42
Karamar Hukumar da dan takarar YPP, Ifeanyi Ubah, ya fito, Nnewi ta Arewa ita ce ya lashe da kuri’a 6,485, yayin da Farfesa Soludo ya sami 3,369.
Kazalika, a Karamar Hukumar Ogbaru ma, dan takarar PDP, Valentine Ozigbo ne ya lashed a kuri’a 3,445, sai APGA da ke biye masa baya da kuri’a 3,051.