Ministan Kwadago da Samar da Ayyuka, Chris Ngige bai samu damar kada kuri’a ba a zaben Gwamnan Jihar Anambra, minti 45 bayan zuwan shi rumfar zaben da ya yi rajista.
Hakan ya faru ne sakamakon tangardar na’urar tantance masu kada kuri’a.
“Na’urar ba ta shaida fuskata ba, aka ce don ban yi murmushi ba ne.
“Na yi murmushi, na ce ‘cheese’ amma ina”, inji Dokta Ngige.
A wannan karon dai Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bullo da wata sabuwar na’ura mai daukar hoton masu son kada kuri’a wadda ake kira BVAS.
Sai dai kuma akwai rahotannin da ke cewa na’urar ta gaza a wurare da dama.
A wasu mazabun ma an ce ba a fara tantance masu zabe ba sai kusan karfe 1:30 na rana saboda tangardar na’urar.
A cewar Dokta Ngige, “Ya kamata a ce INEC ta gwada duk na’urorin akalla mako guda kafin ranar zabe”.
Ministan, wanda ya sha alwashin jira har sai ya jefa kuri’arsa, ya kuma nuna takaici da yiwuwar “hana mutane zabe”.
“Kuri’a daya tana da muhimmanci domin za ta iya kawo sauyi, musamman a zabe irin wannan da za a fafata sosai.
“A wannan rumfar zaben kuma mutum 300 ne suka yi rajista, don haka ba karamar asarar ba ce a ce an rasa kuri’u masu yawa haka”, inji shi.