✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zaben 2023: Kano ta yi sabon Kwamishinan ’yan sanda

An tura masu mukamin CP biyu da DCP uku kwanaki kadan gabanin zabubbukan da ke tafe

A matsayin bangare na shirye-shiryen zaben 2023, Sufeto Janar na ’Yan Sandan Najeriya ya tura sabon kwamishinonin ’yan sanda da mataiman Kwamishina biyu zuwa Jihar Kano domin ayyukan zabe mai zuwa.

Aminiya ta tattaro cewa an tura Kwamishinan ‘Yan Sanda na Kano, CP Mamman Dauda, zuwa Jihar Filato sannan aka maye gurbinsa da CP Muhammad Yakubu.

Kazalika, an tura CP Ita Uku-Udom don kula da shiyyar Kano ta Tsakiya, sannan DCP Abaniwonda Olufemi zuwa shiyyar Kano ta Arewa.

Aminiya ta gano cewa da farko an tura CP Sunday Babaji zuwa shiyyar Kano ta Kudu, amma aka maye gurbinsa da DCP Adamu Isa Ngoji da DCP Abdulkadir El-Jamal, shi kuma aka tura shi Jihar Kaduna.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce lamarin ba a Kano kadai ya tsaya ba, har ma da sauran sassa sabanin yadda wasu daidaikun jama’a ke tunani.

Sauya wa CP Mamman Dauda wurin aiki zuwa Filato daga Kano na zuwa ne kwanaki bayan da Jam’iyyar NNPP ta yi zargin yana dasawa da gwamnatin jihar don tafka magudin zabe.

Haka ita ma Jam’iyyar APC ta yi zargin Kwamishinan ba ya murkushe masu aikata manyan laifuka yadda ya kamata a jihar musamman kuma a tsakanin magoya bayan NNPP.