Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) ta ayyana ranar Juma’a, 4 ga watan Nuwamban 2022 a matsayin ranar da za ta jagoranci taron yi wa kasa addu’a.
A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba, CAN ta ce a ranar ne za ta yi wa kasar addu’o’i domin kauce wa samun rikici a lokacin babban zaben kasar na 2023.
- Zan yi sulhu da kungiyar IPOB —Peter Obi
- Qatar 2022: Rikita-rikitar da aka yi kafin amincewa da Gasar Kofin Duniya a Qatar
Sanarwar ta ce “mun ga ya zama wajibi a wannan lokaci mai cike da kalubale mu gudanar da addu’o’i, kasancewar duk da irin arzikin da Allah Ya huwace wa kasar, har yanzu ba ta kai matsayin da ya dace da ita ba.”
Kungiyar ta ce ta gayyaci dukkanin ’yan takara mabiya addinin kirista a Zaben 2023 da su halarci taron wanda za a gudanar a mujami’ar kasa da ke Abuja.
Sanarwar ta kara da cewa za ta yi amfani da lokacin wajen addu’o’in ganin an samu ci gaban hadin kai na Najeriya, da kuma lalata duk wani shirin yin zagon kasa ga kasar.