Gwamnan Jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar, ya koka dangane da yadda ake fama da rikice-rikicen cikin gida a jam’iyyar APC reshen Jihar da cewa ba za ta kwashe lafiya ba matukar a ci gaba da tafiya haka.
Gwamnan yayin kaddamar da kwamitin rikon jam’iyyar a ranar Juma’a 25 ga watan Disambar 2020, ya ce muddin jam’iyyar ba ta zauna lafiya ba to babu shakka hakan na iya janyo mata shan kasa a zaben 2023.
- Shakatawa ce ta kai ni Amurka ba jinya ba — Gwamna Sule
- Kotu ta daure matar da ta jagoranci yaki da hana mata tuki a Saudiyya
Gwamnan ya bayyana cewa kasancewarsa dan kasuwa, ba zai yi wata asara ba ko da kuwa jam’iyyar ta fadi zabe a Jihar matukar ba a yi aiki da lura ba an daina tayar da fitintinu a cikinta.
Jihar Jigawa na daga cikin jihohin da jam’iyyar APC mai ci a Najeriya ke mulki a jihar, kuma guda cikin jihohin da suke fuskantar barazanar faduwar zaben 2023, sakamakon rikece-rikicen cikin gida da ka iya kaita ya baro ta a zabe mai zuwa.
Gwamna Badaru wanda jigo ne a jam’iyyar APC a matakin kasa da kuma jihar Jigawa, ya lura cewa rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar a yanzu na iya zama babban kalubale da zai janyo mata shan mugun kaye a zaben mai zuwa.