Wani magidanci ta ya tsallake rijiya da baya a harin da Boko Haram ta kashe manoma 43 ya bayyana wa Aminiya abin da ya faru da su a hannun mayakan kungiyar.
Malam Abubakar Yunus wanda kungiyar ta kashe ’ya’yansa biyu a harin ya ce tare da shi aka kama su kuma a kan idonsa aka yanka su.
- Yadda ’yan Najeriya suka fusata da kisan manoma a Borno
- ’Yan Arewa ku kare kanku daga ’yan ta’adda —CNG
- Arewa ta fi ko’ina hatsari a Najeriya —Sarkin Musulmi
Ya ce suna tsaka da aikin girbin shinkafa na mayakan Boko Haram suk ayi musu kofar rago.
“Mutane na aiki a gonakinsu. A gonarmu abun ya fara ne misalin karfe 10.30 na safe lokacin da mayakan Boko Haram dauke da bindigogi sanye da kayan sojoji suka yi mana kawanya.
“A gabana suka yanka ’ya’yana bayan da daya daga cikin mayakan ya tambaye ni matsayin yaran a wurina! Na amsa da cewa ’ya’yana ne.
“Har yanzu ina cikin tashin hankali game da irin wannan rashin imani da aka nuna min”, inji Malam Abubkar.
‘An shafe majiya karfin yankin Zabarmari’
Majiyar Aminiya a garin Zabarmari ta kisan gillar ta kusa shafe matasa da majiya karfin yankin.
“Matasa ne majiya karfi da za su kula da wannan al’umma a nan gaba aka yi wa kisan kiyashi.
“Ba za mu taba farfadowa ba saboda karni guda na al’umma ne sukutum aka shafe aka bar mu tsofaffi, mata da kananan yara masu rauni”, inji majiyar.
Wakilinmu ya ce manoma da suka hada da mata da kananan yara, suna taska da girbin shinkafa ne mayakan suka ritsa su da misalin karfe 9 na safe ranar Asabar, a Zabarmari mai tazarar kilimita 25 daga Maiduguri, hedikwatar Jihar Borno.
Sai daga baya a ranar Lahadi aka samu karin bayani game da yadda aka karkashe rukunin farko na manoman.
Rahotanni sun ce sai da mayakan suka tisa keyarsu da bakin bindiga zuwa wani wuri sannan suka rika yi musu yankan rago da fille kai.
Bayan sun karkashe rukunin farko na manoma 43, sai mayakan suka yi ta banka wa gonakin da ke yankin wuta.
Hakan ya hana jami’an tsaro da ’yan sa kai isa ga wurare masu makwabtaka da Zabarmari domin ganin halin da suke ciki, a cewar majiyoyinmu.
An yi wa manoma kisan kiyashi a Zabarmari
A ranar Asabar ce aka tsinci gawarwakin manoman su 43 bayan kungiyar ta yi musu yankan rago a yankin Zabarmari na Jihar Borno.
Kisan gillar da kungiyar ta yi wa manoman wadanda aka yi jana’izarsu ranar Lahadi ta fusata ’yan Najeriya wadanda suka jaddada kiraye-kirayen a tisa keyar Manyan Hafsoshin Tsaro.
Rahoton Ofishin Majalaisar Dinkin Duniyan na ranar Lahadi ya ce adalin manoman da da aka kashe a harin na Zabarmari, ya karu zuwa 110.
Ofishin ya ce bayan jana’izar 43 daga cikin manoman shinkafar da aka fara gano gawarwarkinsu bayan iftila’in na kauyen Koshebe da ke Karamar Hukumar Jere.
Sai dai kakakin Rundunar Tsaro ta Najeriya, Manjo Janar, John Enenche ya musanta rahoton, inda ya ce mutum 43 ne sojoji da mazauna yankin suka gano gawarwakinsu.
Muna cikin tashin hankali —Zulum
Da yake ta’aziyya ga al’ummar Zabarmari, Gwamna Babagana Zulum, ya ce: “Ina kara jajanta muku game da wannan mummunan rashi da ya same mu baki daya da duk wani mutum mai tausayi.
An shaida min cewa har yanzu akwai wadanda ba a gani ba kuma tun jiya [Asabar] muke magana da sojoji, in Allah Ya yarda za a gano su.
“Abin takaici ne a ce an yi wa fiye da mutum 40 yankan rago daga gonakin da suke aiki.
“Mutanenmu na cikin tsaka mai wuya ta fuska biyu: idan suka zauna a gida yunwa ta kashe su; idan kuma suka je gona Boko Haram ta kashe su.
“Wannan abun takaici ne matuka. Muna rokon Gwamnatin Tarayya ta dauki karin matasan sa kai na CFJT da mafarauta a aikin soja da Civil Defence don a sa su cikin jami’an tsaro masu kare gonaki da manoma.
“Akwai tsananin bukatar jami’an tsaron gonaki kuma matasanmu sun san yanayin yankin; ba mu yanke kauna ba, muna da kyakkyawan fata cewa za a kawo karshen wannan ta’addanci”, inji Zulum.