✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu zamanantar da kasuwancin fim – Iyantama

Aminiya: Me ya jawo aka kafa wannan kwamiti? Iyantama: Wannan kwamiti da aka yi wa lakabi da Kannywood Distribution Network, an kafa shi ne bayan…

Aminiya: Me ya jawo aka kafa wannan kwamiti?

Iyantama: Wannan kwamiti da aka yi wa lakabi da Kannywood Distribution Network, an kafa shi ne bayan nazari da Hukumaar Tace finafinai ta yi gamae da yadda masana’anatar finafinan Hausa ta tara dimbin masu sanya jari a cikin harkar tun daga kan marubuta mawaka masu daukar nauyi jarumai da daraktoci wadanda sun dade suna yin harkar nan, kimanin shekara  28 amma sai ya kasance su ne masu jari amma wasu ne a gefe ke kwashe ribar. Wasu ne ke cin gajiyar abin. A tsarin na kasuwanci a duniya kamfani shi ne mai cin riba fiye da kowa domin shi ke daukar ma’aikata ke zuba jari shi ke biyan haraji da sauransu . Yawancin wadananan kamfanonin shirin fim din sun bi ka’idojin da gwamnati take son su bi, amma ba sa cin riba. Kasancewar Afakallah daya daga cikinmu tun da ya hau yake tunanin ya za a yi masu sana’ar su sami alfanu. Duk da cewa akwai hukumomi irinsu Hukumar Kare Hakiin mallaka, Hukumar Tace finafnai ta kasa wadanda aka dora musu nauyin yaki da masu satar fasaha, amma har yanzu ba a daina satar fasahar ba. Haka kuma duk da cewa muna da kungiyoyi wadanda ya kamata su nema wa finafinan nan mafita, ko kuma idan ma an yi ba ya kai wa gaci, don haka a mastayinsa na wakilin hukuma wanda zai iya tallafa wa, sai ya yi wannan tunanin na samar da kwamitin nan. Kwamitin kuma ya kunshi wakilcin kungiyoyi daban-daban da ke masana’antar tun daga kan ‘yan wasa, masu daukar hoto masu bayar da umarni masu shiryawa da kuma wadanda ke sanya kudinsu a harkar da sauransu.  An yi taro na farko a kan hakan, a lokacin taro na biyu ne aka kafa kwamitin karkashin jagorancina da membobina.

Aminiya: Wane nauyi aka dora wa wannan kwamiti?

Iyantama: An  dora wa kwamitin nauyin lalubo sabbin hanyoyin da za su fadada kasuwancin fim. Yanayin kasuwanci a duniya ya canza. Kasuwancin finafinamu a wuri daya yake, mun saba idan muka yi fim mu dauke shi mu kai shi Kasuwar kofar Wambai daga nan za a tura shi koina a kasar nan ko kuma duniya. Ba mu raina wannan ba, amma saboda yadda kasuwar ta lalace. Babu yadda ana ciniki ta yanar gizo da sinima amma mu tsaya kllum muna juyi a wuri daya wanda kuma ba ci gaba a kasuwancin, musamman da kasuwanicn ya zama sai ana yin shiri da mai fim sannan za a sayar da fim dinsa.

Kwamitin ya gudanar da taruka har sau takwas da membobinsa domin nemo mafita ga harkar kasuwancin fim  yadda za mu tallata hajjarmu a duniya. Na biyu yadda za mu dakile satar fasaha haka kuma Hukumar Tace finafinai ta dora mana nauyin yadda za mu rusa layin da ake yi na finafinai a kasuwar kofar Wambai bisa son zuciya. Yadda za mu gyara tafiyar na hudu akwai kasuwancin tsakanin kasuwannin Jihar Kano da kuma Gwmanatin Nijar wanda an dade ana fafatawa, su Nijar suna tunain finafinai za  su ba su kudin shiga, don haka aka zauna tsakanin Hukumar Tallafa Haja wato Promotion Council da gwamnati game da yadda za a yi kasuwanci tsakanin masana’antar finafinai da kuma gwamanti Nijar. A Nijar suna da gidajen kallo, Sun bayyana cewa idan misali suka sayi fim dinka a naira dari biyu da hamsin, to za su ba ka riba a kan yawan abin da aka samu daga fim din. Yanzu muna kokarin ganin cewa wanann harka ta fara aiki a cikin wanann shekarar.

Aminiya: Ka yi batun satar fasaha wane irin mataki kuke shirin dauka akai?

Iyantama: Kamar yadda aka sani satar fasahar nan ta kasu kashi-kashi. Akwai ‘yan downloading, za ka tarar kamfani ya kashe kudinsa ya yi fim ammA wani ya na can a wani lungu da ‘yar kwamfutarsa ya je kasuwa ya sayi kwafi daya a kan Naara 130 ko 150 ya dora shi akan  kwamfutarsa sai kuma mutane su kai masa waya yana ba su kan Naira hamsim. Ba ya ga wadannan, akwai masu satar fasaha ta hanyar sayen fim suna nuna shi a gidan kallo ba tare da izinin mai fim din ba. Akwai kuma masu sayen fim kwafi daya su je a buga musu da yawa su rika sayarwa. Mun kai wa Kwamishinan ‘yan sanda ziyara inda ya ba mu tabbacin ba mu cikakken goyon baya akan hakan. Ya bayyana mana cewa Sufeton ‘yan sanda na kasa ya yi umarni da a samar da wani bangare na masu yaki da satar fasaha wanda aka tanada don yaki da masu satar fasaha, wadanda za su taimaka wajen kamo masu satar fasahar. Satar fasaha ita ma sata ce wadda ta fi fashi da makami. Doka ta nuna cewa duk wanda aka kama da satar fasaha aka kai shi kotu a kwace gida da motar da ya mallaka a raba wa mutanen da aka sami finafinansa a hanunsa. Idan wanan kwamiti zai yi aiki na kame zai yi ne tare da wadancan ‘yan Sanda, idan mun kamo mutannen nan za mu nuna musu cewa abin da suke yi ba daidai ba ne, sannan mu umarce su su je su biya tara ko kuma a gurfanar da mutum gaban shari’a don biyan hakkin masu hakki. Mun gano cewa wadannan mutane da ke yin satar fashar nan ‘ya’yanmu ne, sai muka ga cewa ba za mu kyale su haka mu dauki hukunci a kansu ba ba tare da sanar da su ba duk da cewa hukumomin tsaro da na hakkin mallaka sun nuna cewa ba sai mun sanar da su ba.  Hakan ya sa muka kira taron masu ruwa da tsaki da suka hada da masu satar fasahar nan da kuma jami’an tsaro daga bangarori daban-daban da masu zuba jarinsu a harkar inda muka tattauna a kan wanan matsala. An nuna musu abin da suke yi ba dai dai ba ne don haka akwai hukunci akan wanda ya taka doka. Mun nuna musu cewa ba mu son a kama kowa ko daure shi, mun fi so mutum ya bi doka a zauna lafiya. Mun yi yarjejeniyar cewa finafinai za su ria fita kasuwa a duk mako.

dan downloading zai sayi kowane fim a kan Naira dari biyar-iyar gaba daya ya zama Naira dubu uku da dari. Mun ba shi dama ya saka a cikin kwamfutarsa idan zai yi cinikin Naira miliyan daya a cikin makonni biyu akan wadanann finafinai da ya saya daga hannunmu ba daga hannun ‘yan kasuwa ba, ribarsa ce ba sata ya yi ba. Abin da muke so kada ya saya a kofar Wambai ko kan hanya ya zo wurinmu ya saya. Wannan dama ce da muka ba su.  A take shugabansu ya yi godiya bisa wannan ci gaba da aka samu. A yanzu haka mun yi nisa wurin tattara yawan masu wanann sana’a ta downloading mu raba takardar shaida yin sana’ar ga dukanin shugabancin kananan Hukumomi don samaun wanann bayani.

Aminiya: Duba da wannan sabon tsari da kuka kawo na yin kasuwanci kai tsaye da masu downloading, ba ka ganin masu kasuwanicn fim za su zarge ku da ganin kamar kun rufe musu kofa a harkar kasuwancinsu ba ko kuma hakan ya ya kashe cinikin fim na CD tunda mutane za su iya zuwa wurin ‘yan downloading su sayi fim akan Naira hamsin?

Iyantama: Ai ita kasuwar CD tuni ta dade da mutuwa saboda ‘yan downloading. Ada idan ka yi fim kana iya sayar da kwafe dubu 300 zuwa 400 amma a yanzu ba ka iya sayar da kwafe dubu 10. Wani ma yana gaya min cewa da kyar ake iya sayar da kwafe dubu biyar. Batun kuma ‘yan kasuwa za su ce mun yi musu kishiya, to su ma ai sun zuba kudinsu su yi fim sun san kasuwar ba ta ja, ‘yan downloading sun kashe ta. Ba a samun komai a ciki. Ina kiransu su kwantar da hankalinsu su ma suna daga cikin mutanen da za su ci moriyar wannan ci gaba da za a samar insha Allahu tunda su ma suna zuba kudinsu a harkar. A banagare daya ma hakan ba zai hana a ci gaba da kasuwancin CD a kasuwa ba saboda mutanen da ke da ra’ayin ajiyewa.

Aminiya: Wane albishir kake da shi ga masu daukar nauyin finafinai wajen inganta kasuwancinsu?

Iyantama:  Muna kokarin sanya finafinan Hausa a yanar gizo yadda za a rika kasuwancinsa ta hanyar amfani da katin intanet. Za mu cire kudin da ka kalli fim daga katinka na intanet. Idan muka zo za mu tarar da dukanin bayanai a kan fim din da mutum ya kalla da suaransu. Abin da muka samu a fim daya da aka kalla ta kafar sadarwa za mu ware wa mai fim hakkinsa, kwamiti shi ma zai ja nasa saboda harkokin gudanarwa. Haka kuma gwmanatin Jihar Kano ta samar da gidajen kallo a dukanin kananan Hukumomi 44 a fadin jihar tare da samar musu da kayan aiki wadanda za mu yi amfani da su wajen inganta kasuwancinmu. Za mu sayar musu da kowane fim a kan naira dubu daya su kuma za su dauki tsawon makonni biyu suna haskawa. Duk abin da mutum ya samu to ribarsa ce. Mun fara tunanin yadda za mu kuma fadada kasuwancinmu har zuwa gidajen kallon da ke kasashen waje. Idan mutum ya yi fim dinsa da ingancin da za a iya dauka akai kasar waje,  wanan kwamiti zai dauke shi ya kai shi a yi kasuwancinsa a can.

Ita kanta kasuwar CD din ma muna kokarin farfado da ita ta hanyar komawa DbD, domin an daina yayin CD a duniya. Wasu kasashen ma yanzu sun wuce DbD sun koma wasu abubuwa daban. Kullun sabbin dabaru na kallo ne ke zuwa. Muna so masu yin fim su rika sanyawa a cikin DbD, sannan su kuma masu saya su daure su rika saye akan Naira 300 ko 350 domin yana da inganci ya kuma fi karko.