✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Za mu yi amfani da na’urorin zamani wajen dakile laifuka a Kano’

CP Dauda, ya lashi takobin yakar laifuka a fadin jihar.

Sabon Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kano, CP Mamman Dauda, ya sha alwashin yin amfani da na’u’rorin zamani domin dakile miyagun laifuka a fadin Jihar.

Dauda, ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatar da jawabinsa na farko ga al’ummar jihar a matsayinsa na sabon kwamishinan ‘yan sanda na 44 a jihar.‘

Kwamishinan ya bayyana cewa a yanzu rundunar ta karbi wayoyin hannu da layukan waya guda 100 daga daya daga masu ruwa da tsaki a kan harkar tsaro wanda tuni suka fara raba su ga Baturan ‘yan sanda a jihar.

Kwamishinan, ya yi kira ga jama’a da su rika taimaka wa rundunar wajen ba ta bayanan duk wata kai wa da komowa a cikin al’umma, haka kuma idan ana bukatar kiran gaggawa jama’a za su yi amfani da su wajen kira.

“Wadannan wayoyi da muka samu jama’a za su yi amfani da su wajen ba mu bayanan sirri.”

Kwamishinan ya bayyana cewa “Duba da cewa Zaben 2023 na karatowa za mu ci gaba da ganawa da shugabannin jam’iyyun siyasa don gannin an yi komai lafiya tun daga farko har karshe.

“Haka zalika, za mu horas da jami’anmu a kan dokokin zabe kamar yadda Babban Sufeton ‘Yan sandan Najeriya, ya tara kwamishonin ‘yan sanda aka yi musu bita, mu ma za mu sanar da jami’anmu a kan abin da muka koyo.”

CP Mamman Dauda, ya ce za su ci gaba da aiki da sauran jami’an tsaro don yakar dukkanin miyagun laifuka, ta hanyar wanzar da zaman lafiya.