✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu rage farashin kayan abinci —Buhari

Shugaban kasar ya kuma yi alkawarin tallafi ga wadanda suka yi asara a ambaliyar Kebbi

Shugaba Muhammadu Buhari ya bai wa ‘yan Najeriya tabbacin cewa kasar ta kusa ganin bayan hauhawar farashin kayan abinci da ake fama da ita.

Ya kuma yi alkawarin tallafa wa mutanen da suka yi asara a ambaliyar da ta yi mummunar barna a Jihar Kebbi inda aka rasa rayuka da dubban daruruwan hektocin gonaki dauke da amfanin gona musamman shinkafa.

A sakonsa na jaje, Buhari ya bayyana kaduwa, yana mai cewa ambaliyar ta kawo nakasu ga kokarin Najeriya na noma wadatacciyar shinkafa da za ta ci a cikin gida da kuma fitarwa zuwa kasashen waje.

“Jihar Kebbi ce jigo a kokarin Gwamantinmu na farfado da harkokin noma; Ina mika ta’aziya game da mamata da kuma jajantawa ga manoman da suka yi asara.

“Zan yi aiki kafada-da-kafada tare da gwamnatin jihar domin tallafa wa wadanda abin ya shafa”, inji shi.

A sakon da ya fitar a ranar Lahadi, Shugaban Kasar ya ce iftila’in ya zo ne a lokacin da manoma da sauran ‘yan Najeriya ke fatan samun amfanin gona mai yawa domin samun saukin hauhawar farashin kayan masarufi.

“Ina tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa tashin da farashin kayan abinci ba mai dorewa ba ne.

“Muna tattaunawa da kungiyoyin samar da abinci domin magance tsawwala farashi da dillalai da sauran ‘yan kasuwa ke yi da ke haifar da hauhawar farashin kayan abinci”, inji shi.