✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu mayar da hankali wajen bunkasa noma a Afirka —Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci shugabannin kasashen Afirka da su mayar da hankali wajen kara bunkasa harkokin noma a nahiyar. A wata sanarwa da Mai…

Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci shugabannin kasashen Afirka da su mayar da hankali wajen kara bunkasa harkokin noma a nahiyar.

A wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Shugaban Kasar, Femi Adesina ya fitar ya ce shugaba Buhari na jawabin ne a Taron Harkokin Noma da shugabannin kasashen Afirka ke halarta a birnin Dakar na kasar Senegal.

Buhari ya yi kira ga takwarorinsa da su rungumi sabbin tsare-tsaren noma domin tabbatar da samar da abincin da zai ciyar da nahiyar har a fitar da shi zuwa ketare.

A yayin da duniya ke fuskantar hauhawar farashin kayan abinci sanadiyyar yakin Ukraine da Rasha, musamman kan alkama da masara, Buhari ya zayyano wasu matakan da ya kamata shugabannin Afirka su dauka domin sauya wannan matsala.

“Ciyar da Afirka wajibi ne. Dole mu tabbatar da cewa muna ciyar da kanmu a yau da gobe da ma kuma nan gaba.

“Abin da za mu fara yi shi ne mu habaka harkokin noma a kasashenmu”, in ji Buhari.

“Wannan na bukatar samar wa manoma abubuwan da suke bukata kamar ingataccen irin shuka da wadataccen takin zamani da sabbin dabarun noma.

‘‘Idan muna son yin nasara dole mu tallafa wa manomanmu, babu shakka akwai bukatar taimaka wa manoma, amma ya kamata mu yi haka cikin gaskiya, mu cire musu dabi’ar neman rance.

‘‘Ya kamata kasashen Afirka su kara azama a bangaren noma a kasafin kudinsu, musamman zuba jari domin samar da abubuwan da ake bukata kamar habaka bincike da samar da abubuwan more rayuwa musamman hanyoyi da noman rani da kuma makamashi,” in ji Buhari.