Gwamnatin Tarayya ta yi barazanar kwace lasisi tare da hukunta duk likitan da ke kin karbar marasa lafiya a asibitinsa saboda tsoron annobar coronavirus.
Ministan Lafiya Osagie Ehanire ya sanar da hakan yayin jawabin hadin gwiwa da kwamitin kar-ta-kwana kan yaki da annobar ya gudanar karo na 42 a Abuja ranar Alhamis.
A cewar ministan, kin karbar marasa lafiya ya saba da dokokin aikin likita, kuma da zarar aka tabbatar da laifin ba za a yi wata-wata ba wajen kwace lasisin likitan.
Ya shawarci duk mara lafiyan da ya fuskanci irin wannan matsalar da ya mika korafinsa a rubuce ga hukumar asibitin ko Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya ko kuma ta jiha idan asibitin mallakin jiha ne.
- Asibitoci na kin duba marasa lafiya saboda tsoron coronavirus
- Yadda ma’aikatan lafiya ke kamuwa da COVID-19 a Najeriya
“Na sha fada a nan wajen cewa ba daidai ba ne kuma saba doka ne a ki sauraron mara lafiyan da ya zo asibiti. Duk wanda ya zo to ya zama wajibi a saurare shi, ko da kuwa da shawara ce.
“Idan akwai wani dalili da zai hana sauraron mara lafiyan, wajibi ne ka fada masa inda zai je ko ma ka kira masa wani ya duba shi. Amma ba daidai ba ne kawai ka yi watsi da shi.
“Amma idan hakan kuma ta faru da mara lafiya, to yana da damar ya rubuta korafinsa ga hukumar asibitin don daukar mataki”, inji ministan.
Ministan ya ce su kan karbi korafe-korafe irin wadannan, kuma duk lokacin da suka samu su kan mika su ga kungiyar likitoci wadda idan ta tabbatar da laifin ta kan hukunta su, hukuncin da a cewarsa ya kan kai ga janye lasisinsu.