✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu kawo karshen matsalar tsaro da talauci a Arewa – Shettima

Mataimakin shugaban kasa, ya ce za a kaddamar da shirin da zai kawo karshen rashin tsaro a Arewa

Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, ta ce za ta kaddamar da wani shiri na magance tashe-tashen hankula da fatara, da sauran kalubalen da ke addabar yan Arewa.

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ne, ya bayyana haka a wata ziyarar ta’aziyya da ya kai Kano.

Shettima, ya je Kano ne domin jajanta wa gwamnati da al’ummar Kano bisa rasuwar dattijon jihar, Alhaji Abubakar Imam Galadanci.

Ya ce, “Shugaban Kasa ya kuduri aniyar yin ayyuka masu tasiri, ta hanyar magance rikicin da muke fama da shi a Arewa Maso Yamma wanda talauci ke kara ta’azzara shi.

“Sai dai idan muna son yin yani ta hanyar amfani da soji don magance rikici a yankin Arewa maso Yamma ba. Dole ne a samo mafita mafi dacewa.

“A cikin makonni biyu masu zuwa, za mu gabatar da tsarin sa zai magance korafe-korafe da rashin zaman lafiya ga ’yan uwanmu na Fulani a yankin Arewa Maso Yamma da kuma magance ayyukan ’yan fashi da tada kayar baya a cikin al’umma,” in ji shi.

Mataimakin Shugaban Kasar, wanda Gwamna Abba Yusuf ya tarbe shi, ya kai ziyara gidan Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero, inda ya yi masa ta’aziyyar rasuwar marigayi Imam Galadanci, tare da mika ta’aziyyar Shugaba Tinubu.

Shettima, a madadin Tinubu, ya jajanta wa iyalan marigayin, ya kuma yi addu’ar Allah ya jikan mamacin.