Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa na kokarin ganin ta kawo karshen fita kasashen waje da ’yan Najeriya ke yi don neman lafiya.
Shugaban ya bayyana hakan ne yayin da yake kafa harsashin ginin bangaren zartarwa na Kwalejin Kimiyyar Lafiya, da ma sauran jami’anta da ke sabuwar makarantar a Otukpo da ke jihar Binuwai.
- Gwamnatin APC ta jefa Najeriya cikin tsaka mai wuya — Kwankwas
- Har yanzu Wike na fama da kuruciya – Sule Lamido
Shugaban wanda ministan Ilimi Adamu Adamu ya wakilta, ya ce ya ji dadin yadda Jami’an gudanarwar kwalejin suke tafiyar da lamuranta, don haka ko shakka babu za su dinga fitar da sahihan Ma’aikatan lafiya, hadi da kawo karshen yawon neman magani.
Ya kuma ce ma’aikatarsa ba ta jima da sahale fitar da Naira Biliyan 3 na tallafi ta Asusun tallafawa Ilimin gaba da sakandare na kasa TETFUND ba, domin habaka tsarin bada ilimi da bincike a makarantun.
A don haka shugaban ya yabawa Ministan Ilimi, da Hukumar da ke kula da makarantun, da ta Jarabawar shiga jami’a JAMB, hadi da ma’aikatar gona, bisa tallafawa sabuwar Jami’a a wajen ciyad da ita gaba domin fara da karatu a shekara dayan da aka kafata.
A nasa bangaren shugaban Kwalejin Farfesa Innocent Ujah ya ce da zarar an kammala bikin bude ta za su l su fara karatu, kafin karewar 2023.