Sabuwar zababbiyar shugabar kungiyar kwadago bangaren Mata ta Jihar Gombe wato NLC Women Wing Rhoda Elias Thomas, ta yi alkawarin shawo kan matsalolin mata a jihar musammam yi wa yara kananan fyade idan ta samu hadin kan matan.
Rhoda Elias Thomas, ta bayyana hakan ne a lokacin da take zanta wa da Aminiya a Gombe jim kadan bayan an zabe ta sabuwar shugabar kungiyar kwadagon bangaren mata.
Ta ce za ta hada kai da gwamnati wajen ganin an samar wa da matan da basa aiki sana’oi don su sami hanyar dogaro da kansu su bar zaman banza wanda hakan ke jefa rayuwarsu cikin garari domin rashin aiki, inda t ace suma suna da hakki a taimaka musu.
Sabuwar shugabar ta ce akwai akalla mata ma’aikata sama da dubu 30 a jihar, inda ta ce don ganin suna samun kulawar da ta dace za ta hada kai da shugaban kungiyar kwadago na jihar Kwamred Haruna Kamara saboda ta san cewa abunda ba za ta iya ita kadai ba idan ta hada kai da shi za su iya samun biyan bukata daga wajen gwamnati.
Rhoda Elias, ta kara da cewa a matsayinta ta shugabar mata ‘yan kwadago za ta zauna da matan ta ja musu kunne kan abubuwa marasa kyau da shugaban kwadago na jiha ya koka akai na yadda wasun su suke mayar da Sakatariyar kungiyar wajen shashanci ta hanyar zuwa suna hirarraki
marasa amfani da mazajen da ba na su ba. Sannan kuma tayi kira da babbar murya ga uwargidan gwamnan jihar Hajiya Ummi Adama Ibrahim dankwambo, da ta ninka irin tallafin da take
basu na kujerun aikin Hajji da Urshalima. A bangaren gona kuwa da yake tana basu takin zamani ta ce akwai mata manoma da yawa a cikin su da suke karuwa, don haka ta ce suna bukatar kari idan da hali.
Daga nan sai ta kara da cewa a bangaren ba da tallafi don karo karatu akwai mata a jihar da dama da suke neman a tallafa musu don su tafi makaranta da fatar za ta ji rokon su dan share musu hawaye.