Shugaban Kungiyar ’yan fansho na kamfanin, Idi Sule ne ya bayyana haka yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai yayin da hukumar fansho ta PTAD ke tantance ma’aikatan wanda aka yi a harabar kwalejin sojoji ta NDA da ke Kaduna.
Ya ce sun yanke shawarar kin janye karar da suka shigar wanda ya hana wadanda suka mallaki kamfanin su sake fasalin kamfanin.
Kimanin Naira miliyan 727 da digo 1 wanda ya yi daidai da kashi 17 cikin dari Ma’aikatar Lafiya ta jihar Kaduna ta saki tsakanin watan Janairu da watan Yuni shekarar 2017 daga cikin Naira biliyan hudu da digo 158 wanda gwamnatin jihar ta warewa ma’aikatar lafiyar jihar.
Hakan na kunshe ne cikin rahoton kasafin kudi na ma’aikatar lafiyar daga watan Janairu zuwa watan Yunin shekarar 2017 wanda hukumar bin diddigi ta jihar ta fitar a jihar.
Rahoton ya nuna cewa hukumar magunguna ta jihar ta sami fiye da Naira miliyan 259 daga cikin fiye da biliyan 1 da aka ware mata, sai kuma hukumar raya asibitocin jihar ta samu fiye da naira miliyan 901 daga cikin fiye da Naira miliyan hudu da aka ware mata.