✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu kamo masu garkuwa da daliban Islamiyya — Gwamnatin Neja

Gwamnatin ta ce za yi amfani da salon da ta yi wajen ceto daliban Kagara.

Gwamnatin Jihar Neja ta bayyana cewa tana bin sahun wadanda suka sace daliban Islamiyya a garin Tegina dake jihar.

Mataimakin Gwamnan jihar, Alhaji Ahmed Mohammed Ketso ne ya tabbatar da hakan ga ’yan jarida a Gidan Gwamnatin Jihar da ke garin Minna.

“Gwamnati na yi kokarin wajen ganin an kubutar da daliban cikin koshin lafiya. Duk da cewar ba a san adadinsu ba, amma jami’an tsaro na bakin kokarinsu kan lamarin,” cewar Ketso.

Gwamnatin ta ce tana duk mai yiwuwa wajen ganin daliban sun kubuta cikin koshin lafiya.

Mataimakin Gwamnan ya kuma kara da cewa akwai makarantu da dama a garin Tegina da aka mayar na jeka-ka-dawo saboda yawan hare-hareb da ’yan bindiga ke kai wa makarantu a jihar.

Ya bayyana takaicinsa kan yadda aka sace daliban Islamiyyar a karshen makon da ya gabata.

Kazalika, ya ba da tabbacin kubutar da su kamar yadda gwamnatin ta yi a baya ga daliban makarantar Kagara ba tare da biyan ko sisin kwabo a matsayin kudin fansa ba.

“Ba ma biyan kudin fansa ga masu garkuwa, muna tattauna da su ta yadda za mu iya kubutar da wanda suka sace,” a cewarsa.

Ya kara da cewa gwamnatin jihar, ta tattauna da wasu daga cikin iyayen daliban, tare da kwantar musu da hankali game da ’ya’yan nasu.