Hukumar ’Yan Sandan Najeriya ta ce za ta dauki matakin da ya dace kan jami’inta, DCP Abba Kyari da ta tadakar, muddin ta same shi da laifin da ake zargin sa da aikatawa.
Hukumar ta yi wannan bayani ne bayan karbar wani rahoto na musamman da kwamitin da ta kafa kan binciken DCP Abba Kyari ya gabatar mata.
- Ana zullumi kan yoyon bututun man fetur a unguwannin Legas
- An kafa kwamitin bincike na musamman kan harin NDA
Babban Sufeton ’Yan Sandan ne ya karbi rahoton kan DCP Abba Kyari wanda aka dakatar bayan an zarge shi da karba rashawa a wajen Hushpuppi, wanda ake zargi da damfara a kasashe.
Rundunar ta kafa wani sabon kwamiti da zai yi nashi binciken kan zargin da Amurka ta yi wa Abba Kyarin wanda ya musanta.
A ranar Alhamis ne Mataimakin Shugaban ’Yan Sanda, Joseph Egbunike ya mika rahoton sai dai ba a bayyana me rahoton ya kunsa ba.
Sufeto Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Usman Baba Alkali ya yi alkawarin hukunta Abba Kyari, matukar aka same shi da laifi.