Wannan ita ce tattaunawar da wakilinmu na Kudancin Kaduna ya yi da Shugaban kungiyar Fulani ta Miyetti Allah na Jihar Kaduna, Alhaji Haruna Usman, a gidansa dake garin Kafanchan. Shugaban na Miyetti Allah ya bayyana irin halin taskun da Fulani suke ciki da kuma kokarinsu na dakile yawon tallar nono da matan Fulani ke yi, domin gyara tarbiyyarsu.
Aminiya: Ka gabatar da kanka ga masu karatunmu
Haruna Usman: Sunana Alhaji Haruna Usman, Shugaban kungiyar Miyetti Allah ta Jihar Kaduna.
Aminiya: Me za ka ce game da zargin sa hannun Fulani a yawancin sace-sacen shanu da kuma yin garkuwa da mutane da ake yi, masu irin wannan zargi su na kafa hujja ne da cewa babu yadda za a yi wanda ba bafulatani ba ya iya tasa garken shanu ya kora su?
Haruna Usman: Gaskiya lamarin akwai takaici kwarai da gaske, domin hakika yawancin sace-sacen shanu ana zargi Fulani ne ke yi, amma a ganina wannan laifin mahauta ne domin idan babu wanda zai sayi shanun da aka sato, (ai ba za a sato ba) domin kuwa ba yankawa za ka yi ka cinye ba. Wannan kuskuren kuma a na samunsa ne ta wajen gwamnati domin kuwa ya kamata a ce idan ka kawo saniya kafin ka sayar da ita ya kamata a ce ka kawo lasisin da zai gwada cewa saniyarka ce kafin ka sayar da ita a kasuwa, shi kuma mahauci kafin ya yanka saniya, sai gwamnati ta san cewa saniyarka ce da ka saya ta hanyar da ta dace, wato akwai rasit, ka ga in ana haka ba yadda za a yi ka sayi kayan sata. To amma yanzu sai ya kasance za a iya tura garke guda a loda su a mota a ratsa jihohi da yawa a kai su Legos ko Fatakwal a sayar, kuma wadannan masu daukar shanun mahauta ne masu sayen dabbobin nan ko nawa ne a wajensu, wannan ne ma ya sa (a satin da ya wuce) muka rubutawa gwamnatin Jihar Kaduna takarda muna neman izininta domin mu tabbatar cewa ba a sayar da shanu sasakai ba tare da gwamnati ta samu kudin shiga, kuma Miyetti Allah ma ta samu kudin shiga ba, kuma ta san ya aka yi aka samo saniya har aka sayar da ita ko aka yanka ba. Ka ga wannan zai taimake mu mu rage irin wadannan ayyukan ta’addancin da ake yi. Shi kuma maganar garkuwa da mutanen na da ake yi a ina aka samo shi, ta ina ya fito! Wannan abin tambaya ne. duk wadannan abubuwa da ake yi suna da shugabanninsu wadanda su ke zaune cikin jama’a kuma suke daure musu gindi kan wadannan abubuwa. Kuma gaskiya tsarin da jami’an tsaro suke bi wajen kama irin wadannan mutane ba sa bin ka’ida, yanzu misali a ce ga shi an yi sace wani an yi garkuwa da shi idan jami’an tsaro suka isa wajen ba su samu masu laifi ba ba sa dawowa sai sun kama wanda bai san hawa ba bai san sauka ba je su yi ta tsare shi su yi ta cutarsa ba, wannan yana daya daga cikin abubuwan da ya dagula al’amarin. Mu mun yi kira ga jami’an tsaro cewa idan an kawo rahoto cewa an sace wani a wuri kaza to su zo muna da ‘yan banganmu na Fulani wadanda za su jagorance su su shiga dajin tare. Wata matsalar kuma ita ce na mutanenmu wadanda suke kan su, gari daya su ke da yaran nan amma ba sa fitowa su fadawa jami’an tsaron cewa ko da an kama yaran bai wuce sati daya ko biyu sai ka ga an sako su kuma idan sun dawo su ka gane cewa ga wadanda suka nuna su, to kashe shi za su yi. Kwanan nan mun aikewa gwamna domin irin wadannan abubuwan gwamnati ba ta sani ba, abinda ake zuwa a fada musu daban, abinda ke faruwa kuma daban. Daga cikin abubuwan da muke son yin doka don mu hana yinsa shi ne yawon tallar nono da matan Fulani ke yi domin akwai illa matuka saboda galibin kangararrun yaran da muke samu din nan, ana samunsu ne ta hanyar da ba ta dace ba. Don haka muka kira Ardodi mu ka gaya musu cewa duk inda Fulani suke saida nono to ya kasance shago ne da suke taruwa duk mai bukata nan zai ya saya, ba wai a dauka a je nan, a je can ba.
Aminiya: Ana danganta fulani da yawancin rikice-rikcen da ke faruwa a kasar nan, ko me ya sa a kowane lokaci su ne abin zargi?
Haruna Usman: wadannan duk yawanci zage-zarge ne kawai. Ka ga kwanakin baya an kai hari a Inugu an ce fulani ne, mu kuma mun fadawa mutane cewa wannan magana ce kawai, ana dai fakewa ne da cewa tunda shugaban kasa bafulatani ne, bari a je a bata bafulatani, a bata gwamnatinsa. Babu wani mahaluki a kasar nan da ya zai ce bafulatani me son tada rikici ne. Mutumin da yake tafiya tare da iyalinsa da dukiyarsa, (bai da asusu a banki), shi ne zai je yana tada rikici? Rashin adalci ne na gwamnatin da ta shude, inda wasu za su taso su kashe mutum ba tare da sun dauki wani matakin da ya dace don hukunta masu aikata hakan ba, shi ya sa suke bi suna ramawa.
Aminiya: To wasu na ganin cewa karewar dabbobi a wajen fulani shi ke sanya wasunsu shiga ayyukan fashi da makami, sace-sace da sauransu, shi kuma me za ka ce kan wannan?
Haruna Usman: Wannan duk zarge-zarge ne kawai. Akwai yaran da aka kama wajen su biyar ko shida duk ’yan gidan masu kudi ne, fitina ce kawai ba talauci ba, in ka lura a zamanin da bafulatani ba zai maka karya ba ballantana ya saba alkawari ko ya dauki wani abu naka ba, amma yau al’amarin ya lalace.
Aminiya: Wanne halin fulanin dake zaune a sassan kudancin Kaduna ke ciki?
Haruna Usman: Tun bayan rikicin 2011 aka watsa fulanin dake zaune aka kokkona wurarensu, amma daga baya muka yi ta binsu muna rokon da su dawo, ga shi yanzu sun daddawo. Sai kuma kiran da muke yi wa gwamnati ta tabbatar wuraren kiwon shanun da aka sansu, to a tabbatar da su domin a zaunar da fulanin nan a karantar da ‘ya’yansu don su samu ilmin zamani da na addini, wannan shi ne zai taimaka mana.
Aminiya: Wanne kira kake dashi ga gwamnatocin jihohi da na tarayya kan yadda za ta magance rikicin makiyaya da manoma da ya ki ci ya ki cinyewa?
Haruna Usman: Ina ganin yanzu gwamnati ta fara daukar don yanzu haka ta ta kafa wani kwamiti da zai ba ta shawara game da wuraren kiwon dabbobin da ake da su domin ganin an samu nasara wanda ni ma ina cikin wannan kwamitin. Insha Allahu kuma za ta yi abinda ya dace.