Louis ban Gaal ya ce da zarar kulob din Manchester United ya doke na Manchester City a gasar rukunin firimiya na Ingila a jibi Lahadi yana da yakinin suna daga cikin kulob din da zai iya lashe gasar a bana.
United dai ta lashe kulob din Eberton ne a ranar Asabar da ta wuce da ci 3-0 yayin da kulob din Manchester City kuma ya lallasa na Bournemouth da ci 5-1. Yanzu haka Manchester City ce take sama a teburin gasar da maki 21 daga wasanni 9 yayin da Manchester United kuma take a matsayi na uku da maki 19 daga wasanni 9.
Morgan Schneiderlin da Ander Herrera da kuma Wayne Rooney ne suka ci wa United kwallaye ukun a karawar United da Eberton.
ban Gaal ya ce harin da suke yi shi ne su zama zakaru, kuma abu ne mai mahimmaci da suke son cimma. Ya kuma kara da cewa ya ji dadi da yadda ‘yan wasansa suka murza leda da kwazon da suka yi, yana mai alfahari da su. Kocin ya kara da cewa ya kamata su dora a kan kokarin da suke yi, “Kuma da zarar mun doke City a wasan gaba, zan gamsu da cewar za mu iya lashe kofin firimiya bana”, in ji shi.
Za a buga wasan ne a gidan United da misalin karfe 3 da minti biyar na rana agogon Najeriya inda ake sa ran dubban magoya bayan kwallon kafa za su kalli wasan a gidan kallo a sassa daban-daban na Najeriya da ma a duniya.