✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu ci gaba da biyan ma’aikatan kananan hukumomi cikakken albashi – Kwamishina

Kwamishinan Kananan Hukumomi da Harkokin Masarautu na Jihar Nasarawa Alhaji Haruna Osegba ya ce gwamnatin jihar za ta tabbatar ta ci gaba da biyan ma’aikatan…

Kwamishinan Kananan Hukumomi da Harkokin Masarautu na Jihar Nasarawa Alhaji Haruna Osegba ya ce gwamnatin jihar za ta tabbatar ta ci gaba da biyan ma’aikatan kananan hukumomin jihar cikakken albashinsu.

Kwamishinan ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu game da fara biyan ma’aikatan kananan hukumomin cikakken albashinsu da gwamnatin jihar ke yi a yanzu bayan ta rika biyansu rabin albashi da dadewa. Ya ce batun biyan ma’aikatan rabin albashi a jihar a yanzu ya zama tarihi sakamakon mataki da gwamnatin jihar a karkashin Gwamna Umaru Tanko Al-Makura ta dauka na fara biyansu cikakken albashi har karshen wa’adinta.

A kan haka ne ma gwamnatin jihar ta yanke shawarar yin amfani da duk abin da ya shigo asusunta daga kasonta na tarayya komai kankantarta wajen biyan ma’aikata cikakken albashinsu ba tare da ta sake komawa gidan jiya ba. Ya ce idan aka samu faduwa ko karanci a kason jihar daga tarayya, gwamnati za ta cika da kudaden da ke asusun ajiyarta ko kuma ta karbo rance idan bukatar hakan ta taso don dai ta tabbatar babu wani ma’aikacin karamar hukumar jihar daya da ke karbar rabin albashi a karshen wata.

Ya ce “Daga yanzu har karshen wa’adin gwamnatin nan muna so ne mu bai wa biyan cikakken albashin ma’aikatan kananan hukumomin jihar nan fiffiko. Hatta manyan ayyuka a jihar nan ba za mu ba su fifikon da za mu bai wa albashin ma’aikatan ba. Mun riga mun sha alwashi cewa daga yanzu rashin isassun kudin shiga a jihar da sauransu ba za su sake shafar albashin ma’aikatan ba. Hasali ma mun yanke shawara cewa daga yanzu ba za mu ma jira wannan kudi ba za mu rika biyansu a kan lokaci kuma cikakken albashinsu ba kamar yadda lamarin yake a baya ba.”

Game da jita-jitar da wadansu a jihar ke yadawa cewa gwamnatin ta dauki matakin kawo karshen biyan rabin albashin  ma’aikatan kananan hukumomin ne don neman goyon bayansu a zaben 2019, Kwamishinan ya musanta jita-jitar inda ya ce, “Gaskiyar lamarin shi ne mun dauki matakin ne bayan mun lura a ’yan kwanakin nan mun samu karin kudin da muke samu daga Gwamnatin Tarayya kuma a yanzu muna jiran wasu kudi daga kudin kulob din Paris zuwa asusunmu. Kuma kamar yadda ka sani  ma’aikatan kananan hukumomi sun yi hakuri da mu sosai a lokacin da muke fuskantar matsalar tabarbarewar tattalin arziki a jiharmu da kasa baki daya inda muka yi ta biyansu rabin albashi. Shi ya sa muka ga ya dace mu fara cika musu alkawarin da muka dauka musu  cewa da zarar tattalin arzikin jihar nan ya inganta za mu rika biyasu cikakken kudinsu.”

Daga nan sai ya gode wa ma’aikatan kananan hukumomin dangane da hakuri da fahimta da suka nuna wa gwamnati a lokacin da suke karbar rabin albashin, inda ya kuma tabbatar musu da cewa gwamnati tana sane da ragowar kudade da suke bin ta kuma za ta biya su nan ba da dadewa ba.

Gwamnatin jihar ta fara biyan ma’aikatan kananan hukumomin jihar cikakken albashinsu ne a watan Nuwamban bana bayan ta dauki sama da shekara biyu tana biyansu rabin albashi da ake kira Percentage payment a Turance. Kuma idan ba a manta ba a makon jiya wakilinmu ya ruwaito yadda ’yan fansho a jihar suka kai gwamnatin jihar kotu a kan wannan batu na rashin albashin ’yan fansho.