Hajiya Madina Dauda Nadabo tsohuwar ma’aikaciyar jarida ce, ta fara aiki a gidan jaridar New Nigeria sannan ta garzayo zuwa tashoshin gidajen rediyo na tarayya da Muryar Amurka inda ta ke aiki har yau. A wannan hirar da ta yi da wakiliyarmu Halima A. Musa, Hajiya Medina ta ce duk da dadewa da ta yi tana huldar aiki da zamantakewa da ‘yan siyasa, ba za shiga siyasar ba. Ku biyo wannan hirar ku ji dalilin da ya sa ‘yar jaridar ta kyamaci siyasa da kuma fatanta ga al’umma bakidaya.
Tarihinki
An haife ni ranar 25/10/1958 a Unguwar Shanu Kaduna, na fara firamare a 1964 a makarantar ‘ya’yan sojoji da ke Kaduna (New Contonmen) har dai na kai aji uku, zuwa 1966 kafin a yi wannan juyin mulkin da ya kawo yakin biyafara a nan Nijeriya, sai mahaifina ya ga ina samun matsala wajen zuwa makaranta sai ya canza mani makaranta na dawo kusa da gida, don makarantar NDA din sai na tsallaka kogi kafin in kai makaranta ga kungurumin dajin itacen mangoro a lokacin, sai ya maida ni LEA ta Unguwar Sarki, ina daya daga cikin masu kokari a wannan makarantar, domin kuwa ina aji uku ni ke yi wa uwata wasika a lokacin, kuma tana alfahiri da ni, mahaifiyata, ta taimaka wajen gina ni.
Mun kai aji shida a lokacin aka zo a na neman ‘yan mata guda ashirin daga makarantarmu da za su yi jarrabawa ta shiga wata makaranta da ake cewa “Our Ladies Secondary School” a titin Independence, Kaduna, a lokacin ana yin aji bakwai ne, a ajinmu maza sun fi yawa, mata da ke wannan aji mu shida ne kacal, sai a ka ce maimakon makarantar ta rasa sai a ka debi mutun shida daga aji shidda aka hada da ‘yan aji bakwai su zama mutum ashirin, nan na samu shiga, sai ya zama mu hudun da aka debo daga aji shidan ne muka ci jarabawar, Ni da Jummai Shedrack, Hauwa Dikko da Rakiya Abba Siri-siri, a lokacin idan ka ci wannan jarabawar ba wai shikenan ba sai an kara yin hira da ke don gwajin fahimtar dalibai. Sai na shiga babbar makarantar, a lokacin masu kwana makaranta ana biyansu, fam bakwai a kowace wata uku, sai babana ya ce ni ina da kanne guda uku, saboda haka ya fi son in yi jeka ka dawo, duk da ina so in rika kwana makaranata da kawayena, dole na bi umurnin mahaifina.
Da na kai aji uku a nan makarantar sai mahaifina ya koma Maiduguri ya bar ni da kawuna tsawon wani lokaci da na nemi komawa wurin iyaye na sai aka maida ni Maiduguri, na gama sakandare a can.
Yaya a ka yi ki ka samu kanki a aikin jarida dumu-dumu?
A lokacin da na gama kwalejin, na dawo Kaduna lokacin idan mutum ya gama babbar makaranta kai babba ne ma’ana ka yi karatu sosai ke nan, sai na fara aikin jarida a “New Nigerian Newspaper” aka kai ni dakin karatu, sai mun karanta mun yi gyara a turance sannan a buga shi a jarida ya fito washe gari. Na yi aiki a karkashin Marigayi Razak Aremu, Marigayi Aminu Abdullahi da ya yi Edita a New Nigerian, shi kuma Razak Aremu shi ne babban Edita, daidai gwargwado kuma sun yaba da irin turanci na.
Watarana a na cikin muhauwara na mata dalibai wanda gidan rediyon tarraya ta Nijeriya ta shirya inda ni ma na shiga, margayi Khaliya Baba Ahmed shine ya jagorancin shirin a Kaduna. Nan da nan ya yaba da yadda na yi, ya ce ko zan zo ne zo ne in yi aiki a radiyo, to da haka ne ya gano ni, ranar da na yi jarrabawa da su a ranar suka dauke ni aiki, na zo rubuta takardar barin aiki a new Nigerian Newspeper, da kyar suma suka yarda na tafi. To wannan shine hanyar da Ubangiji ya kaga mini na ci gaba da kuma cin abinci har yau da na ke muryar amurka.
Wadanne kalubale ki ke fuskanta a matsayin ki na yar aikin jarida?
Kin san kalubalen da mace ke fuskanta a kullum bai wuce tsakanin ta da maza daman mahaifin ta ne, yayyen ta, ko kuma mijinta ko ta ko’ina mace na samun wannan kalubalen, da a kan ce mata an fi son a ganku ba aji ku ba, malamai sun rarrabe a kan wannan wasu malaman sun ce a’a bai kamata a ji muryar mace ba, wasu kuma suka ce a’a in dai mace za ta rike kanta a addinance da kuma rufe al’aurarta kaf to za’a yardar mata ta yi wannan aiki domin ta dalilin wannan za ta iya yada addininta, kuma ai gyara kayanka bai zama sauke mu raba, wanda ya yi maka gyara mai kaunar ka ke nan, sai muka yi kokarin ta wannan hanyar da Allah ya bamu, mu yi ta fadakar da abin da muka sani na zamantakewar dan adam. Don zan ce miki mahaifina ya goyi bayana amma bazan ce miki cikin sauki ba don kuwa akwai kwaba, akwai bugu duk a ciki amma in na ce ina son abu zai shinfida mani sharruda ya gindaya min su kada kuma in tsallaka matukar na bi haka, sai komai ya zo min cikin sauki, shine ya ba ni karfin gwiwa da na kawo wannan lokacin. Kuma na girma tsakanin yayye maza da yawa, saboda baba na ya rike yaran ‘yan’uwa da yawa shi ya sa a lokacin na tashi kamar namiji saboda haka kalubalen mace mai aiki tun na jarida bai wuce maza amma wannan kalubalen nawa na gyara ne.
Me za ki ce ya harzaka ki kika kore a wannan aiki?
To na yi karance-karance da kwasa-kwasai a nan gida da kasashen waje, da na kama aikin, a cikin aikin aka horar da ni. A wannan lokacin, shugaban wannan gidan radiyon shi ne marigayi dahiru Modibbo ba ya wasa da kwarewa, in kana aiki a sashen turanci, za a horar da kai a sashen yin shirye shirye da labarai, wajen daukar labarai a faifai, a wajen yin bayanan abubuwan da ke faruwa kai tsaye. Don haka a yanzu nan dukkan wadannan fannonin ina amfani da su wajen cin abinci shirin da na ke shiryawa na musamman har yau ana sawa duk da na bar gidan rediyon tarayya. Wata rana kwatsan aka ce mazaunin gwamnati za ta dawo Abuja zamanin Babangida sai aka ce za a zabi fitattu wadanda suka iya aikinsu, suna na ne na farko da gidan radiyon Kaduna ta dauka, zuwa 1996 ke nan, lokacin kuma har na kai babbar jami’a, kin ga na zama mai babbar mukami nima, samun nasarar kowa ya dangantaka ne da yadda mutum ya jajirce, yin ya kamata da kuma rike gaskiya.
Ana miki lakabi da mace mai kamar maza, da kuma mai zinariyar murya, mene ne sirrin?
Sirrin shi ne kawai taimako na Ubangiji Allah madaukakin sarki da ya ba ni murya mai karfin gaske don murya ta ba’a rada da ni, sai na tona mutum don kaifin muryaya sai kuma dan kwazo na da kokarina.