✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu biya Samson Siasia daga Dala dubu 60 da muka samu daga CAF – Pinnick

Shugaban Hukumar kwallon kafa ta kasa (NFF) Mista Amaju Pinnick ya ce hukumarsa za ta yi amfanin da kason Dala dubu 60 kwatankacin Naira miliyan…

Shugaban Hukumar kwallon kafa ta kasa (NFF) Mista Amaju Pinnick ya ce hukumarsa za ta yi amfanin da kason Dala dubu 60 kwatankacin Naira miliyan 24 da dubu 600 da ta samu daga Hukumar shirya kwallon kafa ta Afirka (CAF) wajen biyan basussukan albashin da kocin kungiyar U-23 Samson Siasia tare da mataimakansa suke bi bashi.
Samson Siasia wanda yanzu haka yake horar da kungiyar U-23 a Brazil, ya bayyana cewa yana bin hukumar NFF bashin albashin watanni biyar.
Rahotanni sun nuna saura kiris da Siasia ya ajiye aiki a ranar Litinin da ta wuce jim kadan bayan kungiyar U-23 ta doke ta Sweden da ci 1-0 a wasa na biyu a gasar Olamfik.  An ce da kyar da jibin goshi Kyaftin din kungiyar Mikel Obi ya rarrashe shi sannan ya amince ya cigaba da horar da kungiyar.
Kocin ya bayyana takaicin ganin yadda mahukunta kasar nan suke yi musu rikon sakainar kashi musamman a wannan lokaci da suke wakiltar kasar nan a gasar Olamfik a Brazil.  Ya ce abin bakin ciki ne yadda aka yasar da su a Brazil ba tare da an ba su cikakkiyar kula ba.
Rahoton ya ce wadannan kalamai na Siasia ne suka janyo hankalin shugaban Hukumar NFF inda ya sha alwashin share wa kocin hawaye tare da ’yan kwallon musamman ganin yadda suke haskakawa a gasar ta Olamfik duk da halin kuncin da suka tsinci kansu a ciki.
Najeriya dai ta kai matakin kusa da na karshe kwata-fainal ne tun a wasanta na biyu da Sweden bayan ta hada maki 6. A gobe Asabar ne ake sa ran za a fara wasan zagaye na biyu (kwata-fainal) kuma kungiyar U-23 za ta iya haduwa da Brazil ko Denmark ko Iraki da ke fafatawa a rukunin A.