✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu bai wa Ukraine rancen dala biliyan 50 a kadarorin Rasha — G7

Kadarorin Rasha da aka dakatar suna samar da dala biliyan uku a duk shekara a matsayin riba.

Kungiyar ƙasashe bakwai masu ƙarfin tattalin arziƙi ta G7 za ta bai wa Ukraine rancen dala biliyan 50 daga kadarorin Rasha da aka dakatar.

Ana iya tuna cewa ƙungiyar ta G7 haɗi da Tarayyar Turai EU sun ƙaƙaba wa Rasha takunkumai iri-iri a matsayin wani yunƙuri na ganin ta tsagaita wuta a yaƙin da take yi a Ukraine.

G7 ta amince da matakin ne domin taimaka wa Ukraine yaƙar sojojin Rashan da suka mamaye ƙasar.

Shugaban Amurka Joe Biden ya jaddada a amincewa da wannan matakin a wani sako mai karfi ga Rasha, wadda ta yi ta yi barazanar ɗaukar matakan ramuwar gayya mai raɗaɗi.

A taron G7 da aka yi a Italiya, Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky da Biden sun rattaba hannu kan yarjejeniyar tsaro ta tsawon shekaru 10, inda za ta ba da taimakon sojan Amurka ga Ukraine.

Yarjejeniyar dai na da nufin bunƙasa karfin tsaron Ukraine, da karfafa masana’antar tsaronta, da kuma tallafa mata wajen farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasar.

Ƙungiyar G7 da Tarayyar Turai EU sun dakatar da dala biliyan 325 na kadarorin Rasha bayan mamayewar da ta yi wa Ukraine a shekarar 2022, inda suke samar da dala biliyan uku a duk shekara a matsayin riba.

Ana sa ran samun kudaɗen nan da ƙarshen shekara, inda za su ba da rance na dogon lokaci ga ƙoƙarin yaƙi da farfaɗo da tattalin arziƙin Ukraine.