Gwamnan Jihar Kano ya ce gwamnatinsa za ta bai wa masu zuba jarin kasashen ketare cikakken goyon baya domin su zuba jari domin bunkasa kasuwanci a jihar.
Gwamnan Jihar Dokta Abdullahi Ganduje ya yi wannan albishir din ne lokacin bikin bude Kasuwar Baje Koli karo na 38 a jihar da aka yi ranar Lahadin da ta gabata, inda ya ce idan aka samu masu zuba jari cikin harkokin kasuwanci ko shakka babu za’a samu karuwar arziki da bunkasar masana’antu kamar yadda ake gani a kasashen duniya.
Gwamnan wanda ya samu wakilcin kwamishinan ma’aikatar kasuwanci ta jihar, Alhaji Rabi’u Bako, ya ce jihar tana da albarkatun kasa da ake bukata domin sarrafawa a kamfanoni da masana’antu, don haka akwai bukatar samun masu zuba jari ta yadda za’a amfani wadannan albarkatu sosai.
Shugaban Majalisar Bunkasa Kasuwanci da Masana’antu da Ma’adinai da kuma Aikin Gona wato (KACCIMA), Alhaji Umar dan Sulaika ya bayyana cewa ana gudanar da baje koli ne domin a kulla wasu huldar kasuwanci.
Za mu bai wa masu zuba jari cikakken goyon baya – Ganduje
Gwamnan Jihar Kano ya ce gwamnatinsa za ta bai wa masu zuba jarin kasashen ketare cikakken goyon baya domin su zuba jari domin bunkasa kasuwanci…