✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu bai wa bangaren shari’a ’yancin gashin kai — Gwamnoni

Kungiyar gwamnonin Najeriya ta amince za ta bai wa bangaren shari’a na jihohi ’yancin cin gashin kai. Gwamna Kayode Fayose na Jihar Ekiti wanda shi…

Kungiyar gwamnonin Najeriya ta amince za ta bai wa bangaren shari’a na jihohi ’yancin cin gashin kai.

Gwamna Kayode Fayose na Jihar Ekiti wanda shi ne shugaban kungiyar, ya bayyana hakan da cewa za’a fara ba su ’yancin ne a watan Mayun 2021.

Da yake wa manema labarai karin bayani a ranar Litinin, Kayode ya ce an cimma wannan matsaya ne a wata tattaunawa da aka yi da wakilan bangaren zartarwa da na shari’ar da kuma shugaban ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Farfesa Ibrahim Gambari.

Ya kuma jaddada cewa gwamnoni ba su taba yunkurin hana cikakken ’yanci ba ga majalisun dokoki na jihohi da kuma bangaren shari’a, wanda a cewarsa nan ba da dadewa ba za’a aiwatar da wannan lamari.

‘Muna son a bai wa bangaren shari’a ’yancin cin gashin kai’

Majalisar Dattawa Najeriya ta nemi gwamnonin jihohi 36 na kasar da su bai wa bangaren shari’a damar cin gashin kai, ba tare da wata sasantawa ba.

Opeyemi Bamidele wanda shi ne shugaban kwamitin majalisar na bangaren shari’a, ’yancin dan adam da harkokin shari’a, shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai.

Kungiyar ta tsunduma yajin aiki a baya bayan nan tare da shirya zanga-zanga kan gazawar gwamnati na tabbatar da ’yancin cin gashin kan bangaren shari’a.

Bamidele ya ce akwai bukatar a bai wa bangaren shari’a ’yanci domin tabbatar da dimokuradiyya a Najeriya, wanda a cewarsa tabbatar da hakan babu wanda zai ragu da komai.

“Babu wanda zai ragu da wani abu idan aka tabbatar da ’yancin cin gashin kai a matakin jihohi, tun da an yi hakan a matakin kasa.

“Muna neman gwamnonin jihohi sun tabbatar da wannan ’yanci saboda ’yancin bangaren shari’a ba abu ba ne da za’a tsaya ana sasantawa a kai,” in ji shi.

Yadda yajin aikin Kungiyar Ma’aikatan Shari’a ya gurgunta al’amura

Yajin aikin da Kungiyar Ma’aikatan Shari’a na Najeriya (JUSUN) suka tsunduma makonni biyu da suka gabata, ya kassara harkokin shari’a a sassa da dama na kasar bayan sun garkame kotuna.

Ma’akatan suna yajin aikin ne saboda yin kememen da Gwamnatin Tarayya ta yi wajen tabbatar da ’yancin cin gashin kai ga bangaren shari’a ta fannin samar musu da kudade.

A Jihar Kano kamar sauran jihohin Najeriya da dama, akasarin kotunan da wakilinmu ya ziyarta a Sakatariyar Audu Bako ya tarar da dukkansu a rufe sakamakon yajin aikin.

Da yake tattaunawa da Aminiya, Sakataren JUSUN reshen jihar ta Kano, Kwamared Sulaiman Aliyu ya ce sun yanke shawarar garkame kotunan ne saboda bin umarnin uwar kungiyarsu ta kasa.

Ya ce suna yajin aikin ne da nufin tursasa wa gwamnati ta aiwatar da yarjejeniyar da suka cimma tun shekarar 2013 amma Gwamnoni suka yi biris wajen aiwatarwa.

“Ko a kwanan nan sai da Shugaba Muhammadu Buhari ya sa hannu a kan dokar da ta ba da umarnin a biya mu hakkokinmu amma suka yi kunnen uwar shegu,” inji shi.

Sai dai yawancin ’yan Najeriya ba su da masaniya a kan yajin aikin har sai lokacin da suka je harabar kotunan amma suka tarar da su a rufe.

Alhaji Ibrahim Muhammad wani magidancin ne da ya je kotun da nufin ci gaba da sauraron wata kara da ta shafi ’yarsa amma ya tarar da kotun a rufe.

Ya ce kusan wata daya ke nan ya shafe yana jiran ranar sauraron karar kafin yajin aikin ya zo ya yi masa yankar kauna.

“Ban san yau za a fara yajin aikin ba na garzayo kotu saboda yau aka tsayar domin sauraron kararmu.

“Lokacin da na zo na tarar da wani lauya wanda ya shaida min cewa JUSUN sun fara yajin aiki,” inji shi.

Ya yi kira ga gwamnati da kungiyar ma’aikatan kotunan da su sasanta tsakaninsu kasancewar kotuna ne kadai hanyoyin samar da maslaha ga al’umma.

Kazalika, hatta masu sana’o’i a kewayen kotunan su ma sun fuskanci tasgaro bayan da ma’aikatan suka umarce su da su bar wurin.