kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles za ta hadu da Meziko a wasan sada zumunta da ake sa ran zai gudana a ranar 5 ga watan Maris, 2014 idan Allah Ya kaimu.
Kamfanin Soccer United Marketing tare da hadin gwiwar Hukumar shirya kwallon kafa ta Meziko da kuma kamfanin Euroda Sport ne suka dauki nauyin shirya wasan da zai gudana a Geogia da ke Amurka.
Wasan kamar gwajin dafi ne ga kasashen biyu a shirye-shiryen da suke yi na tafiya gasar kofin duniya da za a yi a Brazil a watan Yuni mai zuwa.
A gasar kofin duniya, Najeriya za ta fafata ne a rukunin F da kasashen Ajantina da Iran da kuma Bosnia-Herzegobina yayin da Meziko kuma za ta fafata a rukunin A da kasashen Brazil da Croatia da kuma Kamaru.
Idan za a tuna a shekarar bara kasashen biyu sun hadu a wasan sada zumunta a Amurka inda aka tashi 2-2.
… Za kuma ta hadu da Meziko a ranar 5 ga watan Maris
kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles za ta hadu da Meziko a wasan sada zumunta da ake sa ran zai gudana a ranar 5 ga…