Za a yi wa mawakin da ya yi wakar Najeriya Jaga-Jaga, Eedris Abdulkareem, dashen koda a mako mai zuwa.
Kenny Ogungbe, fitaccen jagoran a masana’antar waka ta Najeriya ne ya sanar da hakan.
- Yaron da ya yi irin ‘Gadar Zulum’ ya ce burinsa shi ne zama injiniya
- Za a dauke wuta tsawon awa 8 a Kano, Katsina da Jigawa —KEDCO
A makonnin baya ne dai Eedri, ya sanar cewa yana fama da ciwon koda kuma ana yi aikin tace jini a wani asibiti a Legas.
Sanarwar da Kenny Ogungbe ya fitar a baya ta ce, “Shugaban Kamfanin Lakreem Entertainment Inc. ya kamu da cutar koda kuma an kwantar da shi a asibitin inda ake mishi aikin tace jini a wani asibiti a Legas.”
Bayan fitar labarin rashin lafiyar Eedris ne abokin sana’arsa, M.I Abaga, ya nema masa taimakon kudade.
A kwanakin baya mawakin ya tura sako a Instagram inda yake bayanin halin da yake ciki na rashin lafiya tare da godiya ga wadanda suka je dubiyarsa da kuma sanar da cewa ya amince da a nema mishi taimako da masoya da abokan arziki domin a gudanar da aikin dashen kodar da za a yi mishi.