Kungiyoyin kwallon kafa biyu da ke murza leda a Ingila, Manchester City da Chelsea, sun samu nasarar yankar tikitin haduwa da juna a wasan karshen na gasar cin kofin Zakarun Turai ta bana.
City da Chelsea za su yi karon-batta ne a filin wasa na Ataturk Olympic da ke birnin Istanbul na kasar Turkiyya bayan nasarar da suka samu ta doke abokan karawarsu a matakin daf da na karshe na gasar Turan.
- Sallah: APC ta raba wa ’ya’yanta shanu 400 a Zamfara
- SEMA ta tallafa wa kauyuka biyar da gobara ta ci a Yobe
Tun a daren Talatar da ta gabata ce Manchester City ta samu nasarar kai wa wasan karshen bayan ta yi PSG lilis a wasan da aka tashi ci 2-0 a Faransa.
Kazalika, ita ma Chelsea a daren Larabar da ta gabata ce ta saita wa Real Madrid hanyar komawa gida bayan ta yi mata duka a Stamford Bridge inda ta zira kwallaye biyu a haduwarsu ta biyu bayan ta farko da aka tashi 1-1 a matakin gab da na karshe na gasar.
Kamar yadda ta kasance a bara yayin haduwar Liverpool da Tottenham, kungiyoyin Ingila ne za su sake haduwa da junansu a wasan karshe na cin kofin Zakarun Turai ta bana.