✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a yankewa masu garkuwa da mutane hukuncin kisa a Taraba

Gwamnan jihar Taraba Arc. Darius Dickson Ishaku, ya rattaba hannu akan dokar hukuncin kisa ga duk wanda aka kama a jihar da laifin yin garkuwa…

Gwamnan jihar Taraba Arc. Darius Dickson Ishaku, ya rattaba hannu akan dokar hukuncin kisa ga duk wanda aka kama a jihar da laifin yin garkuwa da mutane don neman kudin fansa.

Shugaban majalisar dokokin jihar Peter Abel Diah, ne ya gabatar da kudirin dokar inda sauran ‘yan majalisar dokokin jihar suka amince da kaddamar da dokar.

A wannan sabuwar dokar duk wanda aka kama da laifin yin garkuwa da mutane a jihar zai dandana kudarsa.