✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a tono gawar wani mutum daga kabari bayan an yi musayar ta asibiti a Kano

Wata kotun shari’ar Musulunci da ke jihar Kano ta bayar da umarnin tono wani mutum daga kabarinsa mako daya da binne shi bayan an gano…

Wata kotun shari’ar Musulunci da ke jihar Kano ta bayar da umarnin tono wani mutum daga kabarinsa mako daya da binne shi bayan an gano cewa, an yi musayar gawarsa a asibitin Malam Aminu Kano

A wani rahoto da BBC Hausa ta wallafa ya nuna cewa mataimakin shugaban hukumar Hisbah ta jihar mai kula da ayyuka na musamman, Sheikh Muhammad Al-bakri ne ya tabbatar da lamari a yau Talata.

Rahoton ya ce kotun karkashin jagorancin Mai shari’a Sani Yola, ce ta bayar da umarnin a yi wa gawar sutura kasancewar hukumar Hisbah ta roki kotun da ta bai wa asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano umarnin bayar da gawar wani mai suna Abdullahi Obinwa, ga iyalansa domin binnewa kamar yadda addinin musulunci ya tanadar.

Bayan wannan umarni ne kuma aka samu akasi aka musanya gawar da ta wani dan kabilar Igbo mai suna Basil Ejensi.

Hakan ya sa wasu ‘yan kabilar Igbo garzayawa kotun, Ustaz Ibrahim Sarki Yola ya bayyanawa kotun cewa, an yi musu musayar gawa.

Bayan kotun ta saurari jawabinsu sai ta bayar da umarnin a hako gawar .

A cewar Al-bakri, janyewar da shaidu suka yi ne ya sa kotun ta yanke hukuncin bayar da gawar.

Sai dai zuwa lokacin hada rahoton ba a san inda gawar wancan mutumin da hukumar ta Hisbah take da’awar cewa ya musulunta ba.

Amma tuni hukumar ta Hisbah ta ce, sun fara bincike kan lamarin saboda akwai ‘alamun lauje cikin nadi’.

Wasu bayanan kuma na cewa matar mutumin da aka ce ya musulunta wanda kotu ta yi umarnin binne shi bisa tanadin addinin musulunci, ta yi batan dabo.