✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Za a sare bishiyoyi 80,000 a kasar Spain

Bishiyoyin birnin sun yi matukar lalacewar da barinsu zai iya yin mummunar illa ga mazauna birnin.

Hukumomi a Madrid babban birnin kasar Spain na shirye-shiryen sare wasu bishiyoyi kimanin 80,000 wadanda guguwar dusar kankara ta lalata, inji Magajin Garin birnin, Borja Carabante.

Ya bayyana hakan ne ranar Litinin yayin hira da jaridar El Mundo ta kasar.

Mista Borja ya ce bishiyoyin wadanda adadinsu ya kai kusan kaso biyar cikin 100 na ilahirin bishiyoyin birnin sun yi matukar lalacewar da barinsu zai iya yin mummunar illa ga mazauna birnin.

Sai dai dan siyasar mai ra’ayin ’yan mazan jiya wanda kuma shine ke da alhakin kula da harkokin sufuri da na muhalli a birnin ya yi alkawarin cewa za a sake shuka wasu a madadinsu, ko da yake bai fadi nan da yaushe ba.

Guguwar dai wacce aka yi wa lakabi da Filomena da aka yi a farkon watan Janairu ta tawo da wata iska mai karfin gaske kuma ana kyautata zaton ta yi kusan mutane miliyan daya da dubu 600 ta’adi.

An dai rufe wuraren shakatawa da dama a birnin saboda shirin ko-ta-kwana tun da guguwar ta fara, ciki har da wurin shakatawa na Retiro Park dake birnin na Madrid.