Hukumar Kula da Yanayi ta kasar Pakistan ta yi hasashen samun mamakon ruwan sama a Kudancin lardin Sindh ranar Talata da Laraba, da zai haddasa ambaliya.
A hasashen yanayin ya ce akwai yiwuwar samun ambaliya ranar Talata a Kudu maso Yammacin lardin Balochistan, sakamakon toshewar magudanan ruwa.
Haka zalika ita ma hukumar kula da aukuwar bal’o’i ta kasar (NDMA), ta yi makamancin hasashen a Kudancin Balochistan din na tsawon kwana biyar.
Haka kuma ta ce akwai yiwuwar samun wata ambaliyar sakamakon tumbatsar Rafin Kabul da Indus a wadannan kwanakin.
Don haka jukumar ta shawarci masu ruwa da tsaki da su yi kyakkyawan shirin tunkarar lamarin, domin rage asarar rayuka da dukiya da za a iya samu.
Haka kuma ta shawarci makiyaya da su kau da dabbobinsu daga yankunan da ke kusa da Rafin zuwa tsaunuka, don gudun asara.
Daga faduwar damina a ranar 14 ga watan Yuni a kasar dai zuwa yanzu, ambaliya ta yi sandiyar mutuwar mutum 820 da jikkatar 1,315 a lokuta daban-daban.