A yunkurinta na karfafa tsaro da inganta sufurin jiragen sama a Jihar Legas, Hukumar Filayen Jiragen Saman ta Najeriya (FAAN) ta kammala shirye-shiryen sanya fitilun haska filin saukar jiragen cikin gida da ke tashar Jirgi ta Murtala Muhammad.
Aikin, wanda za a fara shi ranar Juma’a, zai dauki tsawon wata uku kafin ya kammalu.
- An sa mata zaga gari da mijinta a kafada bayan kama ta da kwarto
- Rasha ta samu Dala 24bn daga sayar wa China da Indiya iskar gas
Haka zalika FAAN ta bakin, Babban Manajan da ke kula da sashin hulda da kasuwanci Misis Faithful Hope-Ivbaze, ta bayyana cewa filin jirgin sama mai lamba 18l/36R zai dakatar da zirga-zirga a tsawon lokacin.
Sai dai ta bayyana cewa hakan ba zai shafi sauran ayyukan jiragen na yau da kullum a filin ba.
Filin jiragen saman dai an sake kaddanmar da shi ne a shekarar 2006, bayan gyara da aka yi masa, ba tare da an sanya fitilun titinsa ba.
Wannan ya sanya jirage ba sa iya sauka a cikinsa da dare, sai dai a bangaren da aka tanada domin jiragen da ke jigilar kasashen ketare, sannan su dawo bangarensu.
Majalisar Zartaswa ta Tarayya dai tun a farkon shekarar 2022 da muke ciki, ta sahale ware Naira biliyan biyu domin samar wa da kuma sanya fitilun filin jirgin sama na Murtala Muhammadda ke Legas, da na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, da kuma ta Mallam Aminu Kano da ke Kano.